Ɗan jarida, Agba Jalingo, ya bayyana taskun da ya shiga a hannun Abba Kyari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Wani mawallafin jarida mai suna ‘CrossRiverwatch’ kuma ɗan gaba-gaba dai, Agba Jalingo a ranar Litinin da ta gabata ne ya kwance bakin jaka dangane da azabar da ya ɗanɗana a hannun kamammen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da yaransa, lokacin da aka kama shi, haɗi da ɗauko shi tun daga Legas zuwa Kalaba a cikin mota, cikin wani mawuyacin hali.

Ya yi tuni da cewar, an kama shi ne dangane zargin cin amanar ƙasa bisa umarnin gwamnatin jihar Kuros Ribas, kuma an damƙe shi ne a ranar 22 ga watan Agusta na shekarar 2019, kuma aka tsare shi a gidan gyara halinka dake garin Afokang na tsawon kwanaki 179, daga bisani ya samu ‘yancin sa a ranar 17 ga watan Fabrairu, 2020.

Da yake shaida wa wata kafar yaɗa labarai batun kamun nasa a ranar 22 ga watan Agusta, 2019, sai aka tsare shi a wani karɓaɓɓen wuri na fanin IRT dake Ikeja wanda baya cikin hurumin rundunar tsaro ta jihar Legas, kafin a kawo shi garin Kalaba a wulaƙance cikin mota, hannayen sa ɗaure da ankwa, har ma ƙafafun sa an zarge su da ankwa, ba tare da ya kurɓi ruwan sha ba ko kaɗan har isar su garin Kalaba a ranar 24 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar.

A zancen nasa, ya ce, “an kame ni a garin Legas kuma aka ƙunshi ni zuwa wata cibiyar tsaro ta IRT dake Ikeja.  Ni ne na 85 na tsararru da aka tsare a wannan rana, sai kashegari misalin ƙarfe huɗu na Asuba aka jefa ni a cikin ma’ajiyar motar ‘Highlander’ tare da tuƙa ni zuwa garin Kalaba.

“Mun iso garin Kalaba bayan tafiyar awowi 26 a safiyar 24 ga watan Agusta, da farko sun kai ni wani Otal (babu ambatar suna), kuma daga bisani aka miqani wa sashin hana satar mutane.

A wata sanarwa da Agba ya fitar, ya yi zargin cewar, Abba Kyari da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Ubua, gwamnati ce ta biya su aka tsare shi tun daga Legas, kuma sun yi hakan ne a cikin wani wulaqantaccen yanayi domin su daɗaɗa wa wanda ya sanya su yin hakan.