Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Lawal Sa’idu tsohon ɗan jarida kuma wakilin jaridar Peoples Daily a Katsina ya rasu.
Ya rasu da safiyar Alhamis bayan fama da dogon rashin lafiya a Katsina.
Marigayi Lawal Sa’idu ya yi aiki a gidan rediyon Katsina, gidan Talbijin na DITV Kaduna, tsohuwar jaridar Today da Peoples Daily.
Ya kuma riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar ‘yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai (Correspondants chapel) har karo na biyu a Katsina.
Marigayi Lawal Sa’idu ya bar mata biyu da ya’ya da dama.