Daga USMAN KAROFI
Kwamishinan ’yan Sanda na babban Blbirnin tarayya (FCT), Olatunji Disu, ya yi rashin ɗansa, Tunde, a wani hatsarin mota.
Bayanai kan lamarin ba su gama kammala ba a lokacin haɗa wannan rahoto, amma Daily Trust ta tattara cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin, ranar da Kwamishinan ya kai ziyarar ta’aziyya ga CSP A.A. Sambo, DPO na sashin ’yan sanda na Ushafa, wanda shi ma ya rasa ɗansa.
A yayin ziyarar, Kwamishinan ya miƙa ta’aziyya ga CSP Sambo da iyalansa, inda ya yi musu jajen wannan babban rashi tare da ba su tabbacin cikakken goyon bayan rundunar a wannan mawuyacin lokaci.
Da yake jawabi a madadin rundunar ’yan sanda ta FCT, Kwamishinan ya yi addu’ar Allah ya jikan mamacin kuma ya ba iyalansa ƙarfin hali don jure wannan rashin da ba za a iya mayar da shi ba.
A halin yanzu, ƙoƙarin tuntuɓar jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda ta FCT, SP Josephine Adeh, ya ci tura, domin lambar wayarta ba ta shiga ba sau da dama.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba ta maido da martani ga saƙon da aka tura mata ta tes ba.