Ɗan majalisa da gwamnatin Bauchi sun buɗe wa juna wuta kan ruguza gidansa

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazavar ƙaramar Hukumar Bauchi, Hon. Yakubu Shehu Abdullahi, ya bayyana cewar, fashi ne ƙuru-ƙuru da jami’an gwamnatin jihar suka yi na ruguza masa gida mai lamba 7 da ke titin Buba Yero cikin rukunin gidajen gwamnati da ke Bauchi.

A cewar ɗan majalisar, yana da takardar mallaka ta gidan (Certificate of Occupancy) mai lamba BA/39705 da gwamnatin jiha ta amince a ba shi, haɗi da biyan dukkanin kuɗaɗen da ya wajaba ya biya.

Hon. Abdullahi a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar ranar Talata da ta gabata, wacce aka rarraba kwafinta ga manema labarai, ya ce, kuma gwamnatin jiha ce ta amince masa irin tsarin gina gidan, ta hannun hukumar raya birane (Urban Development Board).

Hon. Abdullahi, wanda ya yi jawabi ta bakin sakatarensa, Hon. Ukkasha Hamza Rahama, ya yi watsi da batun cewar, gidansa da aka rusa ba ya cikin rukunin gidajen da wanda ya ke ciki shi zai mallaka (owner-occupier), yana mai danganta wannan bita-da-ƙulli da aka yi masa ga bambancin siyasa da ke tsakanin shi da gwamna.

Ya ce tun lokacin da ya mallaki wannan gida a shekara ta 2018, ba wani taƙaitaccen lokaci da gwamnati ta ƙalubalanci mallakar wannan gida ko da a gaban kotu ne sai yanzu da dangantaka ta lalace tsakanin su, ya ƙara da cewar, zuwa a rusa gidan ma cikin tsakiyar dare yana nuna akwai wani walaki a cikin badaƙalar.
Abdullahi ya yi nuni da cewar, muƙarraban gwamnati sun je harabar wannan gida ne da ake magana a kai ranar 30 ga Satumba, 2021, cikin tsakiyar dare tare da gungun mafarau ta qarqashin jagorancin wani mutum, Umaru A. Maishayi, kuma da zuwansu, sai suka buɗe wuta wa masu gadin gidan inda suka yi masu raunuka, lamarin da ya shigo da taimakon ‘yan-sanda har suka kai su asibiti domin jinyarsu.

“An raunana masu gadin wannan gida a wani yunƙuri na rashin bin doka bisa niyyar a rushe gidan da Hon. Yakubu Shehu Abdullahi ya mallaka, lamarin da ya ke nuni da cewar, rayukan talakawa da Allah ya halitta, da kuma ya kamata gwamnati ta kiyaye ba komai ba ne a wurinta.

“Farmakin da muƙarraban gwamnatin jiha suka kai wa masu gadin gidan da ake magana a kai, an gabatar wa ofishin shiyya na ‘yan sanda da ke cikin rukunin gidajen gwamnati (GRA Area Command) kan wannan batu na rashin ya kamata, kuma batun yana nan tare da ofishin ‘yan sanda da suke bincike a kai.”

Gwamnatin dai ta Jihar Bauchi a nata ɓangaren, ta bayyana cewar, wannan gida mai lamba 7 kan titin Buba Yero ba ya cikin rukunin gidajen da mazaunin sa shi ke mallaka, wato (owner-occupier).

“Akwai tsarin gwamnatin jiha wanda ya bayar da dama, bisa amincewar gwamna, za a iya sayar da gidaje wa mazauna cikin su bisa tsarin, wanda yake ciki shine yake da halin mallaka (owner-occupier). Amma gidajen gwamnati da ke kan titin Buba Yero a cikin rukunin gidajen da ke tsohuwar GRA, waɗanda ake danganta su da Gidajen Kwamishino ni, basu cikin wannan tsari na sayar wa mazauna da ke cikin su,” inji ta.

Mai bai wa Gwamna Shawara Kan Lamuran Gidajen Watsa Labarai da yayata manufofin gwamnati, Mukhtar Mohammed Giɗaɗo, ya shaida wa manema labarai bayan rushe wancan gida da ake magana a kai cewar, duk da wannan hani na sayar da gidajen gwamnati dake kan titin Buba Yero, cikin rukunin gidajen tsohuwar GRA, sai wani tsohon kwamishinan Ayyuka, filaye da Gidaje a wata tsohuwar gwamnati da ta shuɗe, ɗan tsohon Gwamna Alhaji Abubakar Tatari Ali ya mallaka wa kan sa wannan gida da ake batun sa da sunan wani mutum wai shi Mohammed Kabir da ke zaune a cikin ɗaya da ke cikin rukunin gidaje da ke kan titin Ɗanjuma Goje, da ke cikin garin Bauchi.

Giɗaɗo ya bayyana cewar, gidan da ake batun sa, daga bisani sai aka sayar wa Yakubu Shehu Abdullahi, wanda ɗan majalisa ne mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Bauchi, akan jimlar kuɗi Naira miliyan tara.

Ya ce, baicin ƙarya tsarin manufar gwamnati na killace wannan gida daga tsarin mazauni-ma-mallaki, babu kuma wata tsayayyiyar hujja a baital-malin gwamnati ko ma’aikatar gidaje dake nuni da cewar, kuɗaɗen cinikin wannan gida ya shigo wa lalitar gwamnati.

“Ɗaukacin badaƙalar na cinikayyar wai an sayar da wannan gida, ba ta ko kusa da hanyoyin da suka dace, domin babu ma batun fayyace kuɗin gidan shi kan sa, wanda idan cinikin gaskiya ne, farashin sa ba zai kasa Naira miliyan xari ba (N100, 000. 000), bugu da ƙari, babu ma amincewar gwamna na sayar da wannan gida, da ake yin kace-nace a kai.

“Bisa samun rahoto akan wannan gida da majalisar dokoki ta jiha ta yi, wanda gida ne da aka mallaka mata domin ya kasance masaukin baƙin ta, da ma’aikatar shari’a da ta shigo cikin maganar domin wanzar da adalci a tsakani, sai gwamnati ta bayar da umarnin yin bincike dangane da badaƙalar da ke kan wannan gida.

“Kuma a cikin wannan bincike ne na neman bakin zaren, aka gano cewar, shi Hon. Yakubu Shehu Abdullahi da yake tutiyar mallakar wannan gida, har ma ya rushe ginin gidan a ƙoƙarin sa na sabunta shi”.

Ya ce, a bisa la’akari da rahoton kwamitin tsaro ne da aka kafa akan wannan batu, gwamnatin jiha a ranar 30/9/2021 ta tura jami’an ta da suka dace domin ruguza ginin gidan, amma sai aka samu tirjiya daga ‘yan ina ta kwana da Hon. Yakubu Shehu Abdullahi ya yi hayar su, ƙarƙashin jagorancin wani mutum mai suna Ibrahim Ago.
Giɗaɗo ya kammala jawabinsa da cewar, “su waɗannan ‘yan ina ta kwana, da ganin waɗannan jami’ai na gwamnati sai suka buɗe masu wuta, lamarin da ya sanya jami’an na gwamnatin suka ja da baya, bisa aiki da hankali, wanda ya fi aiki da agogo.

A ranar 1 ga watan Oktoba na wannan shekara ta 2021, bayan gwamnati ta gabatar wa hukumar tsaro ta ‘yan sanda rahoton batun lamarin, daga bisani a maraicen wannan rana aka rushe ginin da ke kan wannan gida mai lamba 7 kan titin Buba Yero a cikin rukunin gidajen tsohuwar GRA, Bauchi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *