Ɗan majalisa ya ɗauki nauyin horas da maza da mata kiwon kaji a mazaɓarsa

Daga MUHAMMAD ALI a Gombe

An yi kira ga masu kiwon kaji a Yamaltu Deba ta Jihar Gombe da su tabbata sun ƙwarance akan harkar kafin su tsunduma a cikinta, saboda sana’a ne da take buƙatar natsuwa da tattali.

Ɗan Majalisa mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Dr. Abubakar Yunusa Ahmad Ustaz, ya yi wannan kirar ne a lokacin wani shirin bita na kwana biyu da aka yi wa wasu da suka fito daga mazavar sa, wanda yawansu ya kai 80 wanda ya gudana a ɗakin taro na Quing a GRA dake cikin garin Gombe a jiya Alhamis.

Dr. Abubakar  Ustaz wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa SA, Alhaji Maigari Mega ya wakilta, ya ce wannan shiri ne na musanman, don haka yana mai shawartar waɗanda suka samu horon da su rungumi sana’ar hannu bibbiyu saboda amfaninta. 

Ɗan majalisar sai ya yi fatan alheri ga waɗanda suka samu horon, mata da maza su 80 kuma ya shawarce su da su yi amfani da kuɗin da aka ba su, Naira 50,000 ko wanne ta hanyar da ya dace, musanman wajen bunqasa kiwon kajin su.

A nashi jawabin, shugaban mai’aikatan Hon. Ustaz, wato Alhaji Maigari Mega, jinjinawa ɗan majalisar Ustaz ya yi saboda irin kishin da yake da shi wajen ci gaban mazaɓarsa da al’ummar yankin baki ɗaya.

Ya ce wannan horon na masu kiwon kaji wanda  Hon. Ustaz ya shirya da kan shi, yana da tasiri, saboda zai ƙara ilmantar da waɗanda suka mori gajiyar bitar na kwana biyu yadda yake gudanar da kiwon kaji da yadda za su kiyaye yin asara domin a cewar shi, kiwon kaji baya ga ɗimbin alfanun shi, yana tattare da wasu harsussuka wanda hakan wajibi ne akan duk wani mai son sana’ar, ya samu  horo akai.

“Ganin tasirin da kiwon kaji yake dabshi da kuma irin albarkatun da ake samu a ciki, shine ya sa ɗan majalisar ku mai kishinku, mai hangen nesa, mai kuma taimakon al’umma, wato Hon. Ustaz Ahmad ya ga ya dage yana ta shirya muku irin waɗannan tarurruka domin ci gaban ku. Kuma yanzu aka fara, domin za a ci gaba da irin wannan bitar, inda duk manoman Yamaltu Deba sun amfana,” inji Maigari.

Sai ya ja hankulan waɗanda aka bawa horon da su yi amfani da avubuwan da suka koya ta yadda za su amfana har ma da gwamnati da al’umma baki ɗaya, yana mai  musu fatan alheri a duk inda suke tafiyar da sana’oin su na kiwo.

Shi ma wannan horon wanda Hon. Ustaz Ahmad ya shirya tare da haɗin gwiwar gidauniyar gasa ta ƙasa, wato National Lottery Trust Fund, ya samu halartar baƙi da suka haxa da Alh. Murtala  Muhammad, Alh. Usman Nafi’u da Hon. Abubakar Hassan Difa.

Sauran sun haɗa da Alhaji Maigari Mega wakilin Hon. Ustaz a wajen taron, sai Hon. Habu Dauda, da Musa Omo Difa da Sani Garkuwa da  Garkuwa B Sambo da Ubandoma Mwali da Alh. Adamu Labaran da kuma wakilan Gidauniyar Gasar ta Ƙasa, da suka zo daga Abuja.

Wanda ya yi lakca a yayin horon na kwana biyu, shine Dakta Alex Ambrose, Shugaban Makaranatar Haske Business School da ke garin Gombe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *