Ɗan majalisar wakilai, Alex Ikwechegh, wanda ya ci zarafin direban Bolt yayin da yake isar da kaya gare shi, ya bayar da haƙuri a bainar jama’a.
Ikwechegh ya amince cewa halayensa ba su kai matsayin da ake tsammani ba.
A ranar Litinin, ya bayar da haƙurin, yana cewa, “A matsayina na mai hidima ga al’umma, na fahimci amanar da al’ummar da suka zaɓe ni suka ba ni, da kuma mutanen Nijeriya. Halayena sun kasa kai matsayin da ake tsammani daga gareni, don haka ina neman afuwa sosai.”
“Ina so in tabbatar wa jama’a cewa ina bai wa ‘yan sandan Najeriya cikakken haɗin kai kan binciken wannan lamari. Ina goyon bayan ƙoƙarin su na tabbatar da an yi adalci, kuma waɗanda ke da alhakin haka sun ɗauki nauyin abin da suka aikata,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa ‘yan sanda na Nijeriya bisa tsayawa kan doka da kare haƙƙin ‘yan kasa.
Ya ce, “Ina kuma godiya ga yadda jam’iyyata da ‘yan sanda suka yi tir da abin da na aikata da gaggawa, wanda ya nuna yadda muke tare wurin tsayawa kan doka da kare haƙƙin ‘yan kasa.”
Ikwechegh ya bayyana cewa yana ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalolin da suka haifar da wannan lamarin.
“Ina neman shawarar ƙwararru don tabbatar da cewa irin wannan hali ba zai sake faruwa ba. Haka kuma, zan gudanar da ayyukan taimakon al’umma da suka mayar da hankali kan girmama mutane, tausayi da fahimta.”
Ya kuma kira ga ‘yan Nijeriya su haɗa kai da shi wurin yaɗa al’adar mutunta juna, haƙuri da fahimta.
“Dole ne mu yi aiki tare don gina al’umma inda kowa zai kasance cikin girmamawa da daraja. Na gode da fahimtarku kuma ina fatan zaku shiga tare da ni a wannan tafiya ta warkarwa da ci gaba,” in ji Ikwechegh.