Ɗan Majalisar Wakilai mai jiran gado, Isma’ila Maihanchi ya riga mu gidan gaskiya

Zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai na shiyyar Jalingo/Yorro/Zing a Jihar Taraba, Isma’ila Maihanchi, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne da safiyar Asabar a Abuja bayan fama da rashin lafiya.

Kakakin Jam’iyyar PDP, Andeta’rang Irammae, shi ne ya sanar da rasuwar.

Ya ce, “Jim kaɗa bayan kammala zaɓen marigayin ya fara rashin lafiya wanda ya ci gaba da karɓar magani a Abuja” inda Allah Ya yi masa cikawa ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *