Ɗan Marigayi Gaddafi, zai tsaya takarar shugabancin Libya

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Ƙasar Libya ta sanya ranar 24 ga watan Disamba mai gabatowa domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa karo na farko tun bayan mummunar tashin-tashina da tawaye na shekara da shekaru da ya yi sanadiyyar tunɓuke shugaba Mamman Gaddafi daga ƙaragar mulki a shekarata 2011.

Seif Al-Islam an yi masa gani na farko tun bayan garƙame shi a maɓuya da dakarun yaƙin neman ‘yanci suka yi a garin Zintana ranar 19 ga watan Nuwamba ta shekarar 2011, kamar yadda kafar watsa labarai ta ‘Ammar El-Darwish/AP’ ta ruwaito.

Seif Al-Islam Gaddafi ya yi rajistar tsayawa takarar zaɓen shugabancin ƙasar ne a ranar Lahadi da ta gabata a babban birnin ƙasar ta Turabulas domin tsayawa zaɓe na watan Disamba, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasar ta zayyana.

“Seif Al-Islam Gaddafi dai ya miƙa takardun sa na takarar neman shugabancin ƙasar ga Hukumar Gudanar da Zaɓe ta Ƙasar a birnin Sebha da ke kudancin ƙasar,” bayanin hukumar zaɓe ta ƙasar.

Ta ce ya cika dukkan ƙa’idoji na shara’a domin tsayawa zaɓen kuma an mallaka masa katin jefa ƙuri’a na gundumar Sebha ta ƙasar Turabulus.

Zaɓen shugaban ƙasar Libya na farko a cikin tarihi, wanda za a yi zagayen farko na zaɓen ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa, shiri ne da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar a shekarar da ta gabata domin jan layi daga shekarun da suka shuɗe na hargitsi da tawaye da suka zama majadalar tunɓuke Gaddafi daga kujerar shugancin ƙasar a shekara ta 2011.

Ƙuri’u da ake jira har yanzu suna fuskantar ƙalubaloli, haɗi da wasu batutuwa da suka jiɓanci dokokin zaɓe, dama yin faɗa jefi-jefi tsakanin waɗanda suka sha ɗamarar yin gwagwarmayar rayuwa. Wasu naƙasun kuma sun haɗa da zaman doya da manja da ake yi tsakanin gabaci da yammacin ƙasar da yaƙin basasa ya haddasa, haɗi da tarin dakarun ƙetare da suke jubge a cikin ƙasar ta Libya.

A wata na’urar ɗaukar hoto da ofishin zaɓe ya bijiro, yana nuni da Seif Al-Islam da ya ke sanye da rigar gargajiya, haɗi da rawani da tabarau a fuskar sa yana jawabi inda ya ke cewa, “Allah ne zai samar wa ƙasar ta Libya mafita.”

Seif dai mutum ne da kotun duniya ta ICC ta ke nema ruwa a jallo bisa laifukan cin mutuncin ‘yan ƙasa a shekara ta2011.

Seif Al-Islam, mai shekaru 49 a duniya, shi ne babban ɗa na biyu a cikin ‘ya’yan Gaddafi guda takwas, an yanke masa hukuncin kisa ne a watan Yuli na shekarar 2015 bisa laifukan kisan jama’a a tashin-tashina na shekarar 2011. An sake shi daga gidan jarun na Ƙasar Libya a shekara ta 2017. Seif dai ƙwararre ne matuƙa gaya kan kawo chanje-chanje a zamantakewar al’umma.

Kusan dukkan ‘ya’yan Gaddafi guda takwas, kowanne ya taka wata rawa a tafiyar da mulkin mahaifin su. Ɗan Gaddafi Muatassim, an kashe shi ne lokacin da aka cafke mahaifin. ‘Ya’yan sa biyu Seif Al-Arab da Khamis kuma an kashe su ne a cikin gwagwarmayar mulki. Wani ɗan, Al-Saadi Gadhafi an sake shi daga ɗaurin shekaru bakwai a garin Turabulus, bayan da aka titso ƙeyar sa daga Ƙasar Nijar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *