Wata mata mai shayarwa ta rasu bayan da wani ɗan sanda ya ɗirka mata harbi a bakin titi.
Ɗan sandan ya harbe matar be a bisa kuskure a lokacin da ya buɗe wuta a ofishin ’yan sanda na Oke Ila a garin Ado Ekiti, fadar Jihar Ekiti.
Ɗan sandan ya kai ziyara ofishin ne daga wata shiyya domin taya abokan aikinsa murnar samun ƙarin girma.
A garin haka ne ya yi harbi, wanda harsashi ya sami matar da ke gefe hanya daga tsallaken titi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, wanda aka yi wa ƙarin girma a kwanan nan, AIG Adeniran ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, an kwace bindigar ɗan sandan kuma a halin yanzu yana tsare ana gudanar da bincike.