Ɗan sanda ya bindige mutum don ya ce APC za ta lashe zaɓen gwamna a Filato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani jami’in ɗan sanda ya harbe wani mutum mai suna Nyommena Salah Badapba a lokacin da suke taƙaddamar siyasa a unguwar Tudun Wada da ke garin Jos a Jihar Filato.

Ɗan sandan, Solomon Damak, ya harbe Badapba ne a lokacin da suke muhawara kan wanda zai fito a matsayin wanda zai lashe zaɓen gwamna da za a yi ranar 11 ga watan Maris.

An tattaro cewa, jami’in ya ce jam’iyyar APC ba za ta ci zaɓe mai zuwa ba, amma Badapba ya ƙi amincewa da shi.

Ɗan sandan ya fusata da hakan, sai ya harbi Badapba a ƙafadarsa. An ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 5 ga Maris, 2023.

Tuni dai rundunar ’yan sandan jihar Filato ta kama ɗan sandan da laifin yayin da wanda aka lamarin ya shafa ke jinya a asibitin koyarwa na jami’ar Bingham Jos.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Alabo Alfred, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin 6 ga watan Maris, ya bayyana matakin da ɗan sandan ya ɗauka a matsayin rashin ɗa’a.

Rundunar ’yan sandan ta tabbatar wa da jama’a cewa Kwamishinan ’yan sandan ɗan sanda ne mai cikakken iko wanda ke yin aikinsa da tsoron Allah don haka ba zai amince da duk wani nau’i na rashin ɗa’a da wani jami’in rundunarsa zai yi ba, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

CP ya kuma ba da tabbacin cewa ba za a tauye tsarin ladabtarwa ba kuma za a bayyana sakamakon da aka yi a bainar jama’a.

Ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu kuma su ci gaba da bin doka da oda domin rundunar tana yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Filato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *