Ɗan sanda ya kashe kansa bayan bindige matarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani ɗan sanda ya kashe kansa bayan da ya harbe uwar gidansa har lahira a garin Ilorin na Jihar Kwara.

Mummunan lamarin ya faru ne a Chapel Redemption, UMCA, yankin Agba Dam na cikin garin Ilorin, a ranar Alhamis, 2 ga Maris, 2023.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun sanar da cewa ɗan sandan ya aikata wannan aika-aika ne a kan batun wani yaro da ya taso a danginsu.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa da dawowarta makarantar da yaronta, ɗan sandan ya kama matar da aka kashe, kuma sun tattauna da ita kafin ya harbe ta har sau biyu.

Ya ƙara da cewa nan take ɗan sandan ya harbe kansa har lahira.

Wani ganau da ya ga lamarin daga wani gini da ke kusa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Wani magidanci da ke iƙirarin cewa shi ne mai gidan hayar, ya ce ɗan sandan da matar sun ɗauki hayar wani gida a wurinsa makonnin baya, kuma sun kasance kamar tantabaru a soyayya har suka fara samun matsala tun kwanaki biyar da suka wuce.

“Suna da matsala tun kwanaki biyar da suka gabata. Lolacin da muka ba su hayar gidan, muna jin daɗin yadda suke nuna ƙauna ga juna.

“Wasu sun ce ɗan sandan abokin matar ne, amma sun yi ta rigima tun ‘yan kwanakin da suka gabata,” inji mutumin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da cewa wani dan sanda ya kashe wata mata da kansa ranar Alhamis a Ilorin.