Wani ɗan sanda a Jihar Kwara ya tuttula kashi a wando bayan ya yi tatil da barasa.
Wani faifan bidiyo da aka yaɗa ya nuna yadda jami’in ya tsula fitsari da tuttula kashi a wando alhali yana sanye da kayan aiki, yayin da abokan aikinsa biyu ke ƙoƙarin tallabo shi.
Tuni Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kwara, Paul Odama, ya ba da umarnin a tsare Yohanna don gudanar da bincike.
Da yake tsokaci kan batun, CP Paul Odama, ya nuna ɓacin ran rundunar kan abin da jami’in ya aikata, tare da bayyana lamarin a matsayin abin ƙyama.
A cewar Kakakin ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, “Bayan kallon bidiyon, Kwamishinan ya ba da umarnin a binciko jami’in sannan a tsare shi.”
Ya ƙara da cewa, an gano jami’in, kuma ana ci gaba da binciken lafiyarsa don gano ko yana fama da lalurar taɓin hankali.