Ɗan Sani Abacha, Abdullahi ya rasu a cikin barci

Daga BASHIR ISAH

Ɗan tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Sani Abacha, Abdullahi Abacha, ya rasu yana da shekara 36.

‘Yar uwar marigayin, Gumsu Sani Abacha, ita ce ta ba da sanarwar rasuwar ta shafinta na Tiwita a ranar Aasabar.

Kazalika, majiya daga ahalin marigayin ta tabbatar da rasuwar Abdullahi, inda ta ce marigayin ya rasu ne a cikin barci a gidansu da ke Nelson Mandela Street, Abuja.

“Lafiyarsa ƙalau a daren jiya, amma da safiyar nan sai gawarsa aka tarar,” in ji majiyar.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar za a yi jana’izar marigayin da ƙarfe 4 na yammacin Asabar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

An haifi marigayin ne a 1987, kuma ɗaya daga cikin ‘ya’ya tara da marigayi Sani Abacha ya mutu ya bari.