Ɗan Senegal ne ya lashe kyautar adabin Faransanci

Daga AISHA ASAS

Mohamed Mbougar Sarr matashi daga Ƙasar Senegal ne ya yi nasarar lashe gasar rubuce-rubuce na adabin harshen Faransanci mafi girma wanda ake kira da ‘Concourt’.

Matashin ya yi nasarar cin wannan gasar ne ta sanadiyyar littafinsa mai suna ‘La plus secrète mémoire des hommes’.

Kwamitin alƙalanci na gasar sun jinjina wa namijin ƙoƙarin da Muhammad ya yi a littafin, tare da nuna muhimmancin rubutu irin na littafin ga adabin na Faransanci. Ɗaya daga alƙalan ya yi bita dangane da abubuwan da ke kunshe a wannan littafin na ‘La plus secrète mémoire des hommes’, don ƙara tabbatar da cancantar sa.

Da yake jawabi, gwarzon gasar, Mohamed Mbougar Sarr, ya bayyana farin cikin sa kan wannan nasara da ya samu. Ya kuma ƙara da bayyana kyautar tasa a matsayin muhimmin saƙo da ya fito daga Hukumar Raya Harshen Faransanci zuwa ga marubuta a cikin harshen Faransanci.

“Wannan tukuici muhimmin saƙo ne daga Hukumar Raya Harshen Faransanci zuwa ga mutane da dama, musamman zuwa ga marubuta a cikin harshen Faransanci.” Inji shi.

Muhammad ya ci gaba da cewa, “ina so mutane su fahimci cewa, wannan tukuici ana bayar da shi ne domin cancanta, babu ƙabilanci a ciki. Don haka ba wai na zama zakaran gasar ba ne don na fito daga nahiyar Afirka, sai saboda muhimmancin rubutun da ke ƙunshe a wannan littafin da na rubuta.”

Daga ƙarshe, Sarr ya bayyana gasar a matsayin ta adalci da babu siyaya a ciki. Ya ƙara da godiya da kuma jinjina ga kwamitin alƙalanci na wannan gasar, akan namijin ƙoƙarin da suka yi na ganin sun tabbatar da adalci a zaɓen gwani na gasar.