Ɗan shekara 44, Bassirou ya lashe zaɓen Senegal

  • Shugaba Sall ya taya Bassirou murnar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Bassirou Diomaye Faye ɗan shekara 44, ya zama sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Senegal bayan da ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ƙasar.

Tuni dai Shugaban Ƙasar mai narin gado, Mavky Sall ya taya Bassirou murnar lashe zaɓen.

Bayan ayyana shi a matsayin sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Senegal, Bassirou ya yi wa ‘yan ƙasar bayani game da abubuwan da za su sa ran gani bayan ya karɓi ragamar mulkin ƙasar.

Haka nan, ya ce gwamnatinsa za ta yi tafiya ne cike da tsare-tsare masu inganci ba tare da harigido ba.

Yayin jawabin nasa gaban dubban magoya bayansa da masu ruwa da tsaki, Faye ya ce abin da zai fara sanyawa a gaba, shi ne tabbatar da haɗin kan jama’ar Senegal da kuma ‘yan siyasa, duba da yadda zukatan mutane da yawa suka ɓaci saboda yanayin yadda zaɓen yazo.

Faye ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasar mai barin gado, Macky Sall, wanda ya ce ya yi ƙoƙari matuƙa ganin yadda ya bar ‘yan ƙasa suka zaɓi wanda suke so ya jagorance su.

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta taɓa mantawa da waɗanda suka rasa rayukansu a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da dimokraɗiyya a ƙasar, yana mai cewa waɗannan mutane su ne cikakkun dakarun dimokraɗiyya.

Kazalika, ya ce ba zai watsa wa ‘yan ƙasar da suka amince da shi ƙasa a idanu ba, don haka zai tabbatar da samar da sauƙi kan tsadar rayuwa da ake fama da ita, tare da kira ga ƙasashen Africa da ƙungiyar ECOWAS da su bai wa gwamnatinsa dukannin haɗin kan da take buƙata.