Ɗan shekara 78 ya kashe ɗan shekara 95 kan abin duniya

Daga WAKILINMU

Wani tsoho ɗan shekara 78 mai suna Moshood Habibu, ya shiga komar ’yan sanda bisa laifin halaka ɗan uwansa Salisu Surakatu mai shekaru 95 kan rikicin fili a jihar Ogun.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar cikin makon nan.

Ta bayyana cewa, Moshood ya sara wa yayansa adda har lahira ranar Laraba a Mowe, ƙaramar hukumar Obafemi Owode.

Ta ce, “an damƙe shi ne bisa ƙarar da wani Aminu Tajudeen ya shigar ofishin ’yan sandan Mowe cewa, Salisu Surukatu, wanda aka kashe mahaifinsa kuma wanda ya kashe ya shigo gidansu ne a ƙauyen Kara Ewumi a Mowe inda ya sassareshi kan rikicin fili.”

“Yayin da muka yi wa wanda ake tuhuma tambaya, mutumin ya ce marigayn ya sayar da filin dangi ne kuma ya hana shi nasa kason kuma hakan ya sa yaje kwaton haƙƙinsa inda suka kaure da faɗa.”

DSP Abimbola ta ce, bincike ya nuna cewa, ƙanin ya tafi gidan yayansa da adda. Kasancewar yayan na sa ya makance, bai san yana riƙe da adda ba.

Yayin da marigayin ke faɗa masa ya fita masa daga gida, kawai sai Habibu ya dava masa sara sai da ya daina numfashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *