Ɗan Shugaba Buhari ya fice daga Jam’iyyar APC

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Daura, Sandamu da Mai’Adu’a kuma ɗa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wato Fatuhu Muhammad ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki.

Bayanin haka yana ƙunshe ne cikin wata takarda da ɗan majalisar ya rubuta wa majalisar wakilai ta ƙasa don sanar da ita matakin da ya ɗauka.

Takardar wadda aka rubuta tun 13 ga watan Yuli, 2022 amma ba a fitar ba sai ranar 7 ga watan Agusta, 2022.

A takardar da aka raba wa manema labarai a birnin Katsina, Hon. Fatuhu ya bayyana cewar daga ranar 13 ga watan Yuli shi fa ba ɗan Jam’iyyar APC ba ne, inda ya bayyana jingine katinsa na jam’iyyar mai lamba KT/DRA/10/0002.

Hon. Fatuhu ya kasance ɗan yayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kuma Shugaba Buharin ne ya riƙe sa bayan da mahaifinsa ya rasu shekaru da dama da suka wuce.

Sai dai ɗan majalisar bai sanar da sabuwar jam’iyyar da zai koma ba a yayin da masu sharhi akan al’amuran siyasa ke alaƙanta barin jam’iyyar ta sa da faɗuwa zaɓen fidda gwani da ya yi a zaɓukan da jam’iyyar ta gudanar don fitar da waɗanda za su yi wa jam’iyyar takara a matakai daban-daban.

Daga ƙarshe ɗan majalisar ya gode wa jam’iyyar ta APC bisa damar da ta ba shi na wakiltar mazaɓun ƙananan hukumomin Daura da Sandamu da kuma Mai’adua a zauren majalisar dokoki ta ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *