Wani da ake zargin ɗan Boko Haram ne ya yi ƙunar baƙin wake inda ya tada bom ya kashe kansa a Kaduna.
Bayanan da Manhaja ta kalato sun ce, ɗan ta’addan ya kashe kansa ne gudun kamun jami’an tsaro.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin a ƙauyen Keke, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta rawaito.
Kakakin ‘yan sandar jihar, Muhammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hakan.
Majiyar News Point Nigeria ta ce, da ma ɗan ta’addan na daga jerin ɓata-garin da jami’an tsaron yankin ke nema ruwa a jallo.
Majiyar ta ƙara da cewa, bayan da suka samu labarin maɓuyar ɗan ta’addan aka tada tawagar jami’an tsaro suka kai masa samame.
Ta je ganin jami’an tsaro sun matse shi babu hanyar gudu, ya sa ya tada abu mai fashewa ya kashe kansa.
An ce an gano bindiga ƙirar AK-47 da abubuwan fashewa a ɗakin nasa, sannan an tattara sassan jikinsa da bom ya tarwatsa.
Kazalika, matarsa da ‘ya’yansa na hannun hukuma don ci gaba da bincike.