Ɗan takarar da Gbajabiamila ke son ya gaje shi barazana ce ga dimokuraɗiyyar Nijeriya – Hon. Nalaraba

Daga SANI AHMAD GIWA

Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya bayyana cewa shirin da ake zargin Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila na yi na ɗora Hon. Abbas Tajuddeen a matsayin wanda zai gaje shi a Majalisar Wakilai ta 10 yana da haɗari ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, kan zargin dambarwa da ake yi wa ɗan takara a tsarin dimukoraɗiyya, inda ya bayyana hakan a matsayin savani, rashin bin tsarin dimokuraɗiyya, mulkin kama-karya da kuma babban hatsari ga dimokuraɗiyya, savanin ɗan takararsa, Honorabul Mukhtar Aliyu Betara da ba shi da tsara.

Honorabul Nalaraba wanda ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazavar Awe, Doma da Keana, ya bayyana cewa, “‘yan majalisar wakilai masu bin tsarin dimokuraɗiyya ne waxanda aka zava a jam’iyyun siyasa masu rijista.

“Al’ummar mazaɓarmu ne suka zaɓe mu, mun zavi shugabanninmu da za su yi ka don ci gaban ƙasar nan, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin mun bar abokin aikinmu wanda ba a san shi ba, bai kuma da wani tasiri ga mutanen da ke kewaye da shi shi, kuma wanda a fili ya nuna ba ya son takara a tsakanin abokan aikinsa, amma yana son a ɗaukaka shi kan ‘yan dimukuraɗiyya,” ya ce.

Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya ce shi da mafi yawan waɗanda suka dawo, da sauran sabbin ‘yan Jam’iyyar APC da waxanda ke wajen Jam’iyyar APC, masu cikakken biyayya ne, za su goyi bayan Honorabul Mukhtar Betara a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai ta 10.

Ya ce wasu daga cikin halayen Betara sun haɗa da goyon bayan magoya bayansa kusan 200, ya kuma bayyana cewa da za a lissafa, Betara bai tava jinkirta zartar da kasafin kuɗi ba tsawon shekaru, kasancewarsa Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai; haɗin kan mambobin kwamitinsa da ba a ba su shugabancin wasu kwamitocin ba, wanda ya tabbatar da zaman majalisar; Yana da kunnen sauraro da amsar koke daga mambobi da ma’aikata; Ya tabbatar da zaman majalisar kan duk wata matsala ko barazanar tsige Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila da dai sauran halaye daban-daban saɓanin majalisun da suka gabata.

Sai dai ɗan majalisar ya yi kira ga dukkan ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su mara wa Honorabul Mukhtar Betara baya domin a zave shi a matsayin Shugaban Majalisa domin ya ci gaba da kafa dokokin da za su kawo cigaba da ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *