Ɗan takarar gwamna da magoyabayansa sun sauya sheka a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon Sakataren gwamnatin Jihar Katsina a gwamnatin Aminu Bello Masari kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC, Mustapha Muhammad Inuwa, ya sauya sheƙa zuwa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Inuwa wanda babban jigo ne a APC ya sanar da kwashe kayansa daga jam’iyyar lokacin da yake yi wa ƙungiyoyin dake goyon bayan tafiyar siyasarsa jawabi a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake birnin Katsina.

Inuwa wanda ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Ilimi a jihar, ya ce ya bar jam’iyyar ne saboda yadda aka mayar da shi saniyar ware a sha’anin tafiyar da siyasar jihar.

“A yau ni da ƙungiyoyi 627 dake goyon bayana mun bar jam’iyyar APC zuwa PDP saboda Jam’iyyar APC da wanda zai yi wa jam’iyyar takara (Raɗɗa) ba sa buƙatar mu,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, shugabannin jam’iyyar na sukar shi da ƙungiyoyin dake goya masa baya, suna kuma yi wa dukkan waɗanda ke cikin tafiyarsa barazanar za a ɗauki mataki akansu.

Ya ce, ana yi wa mutanen sa waɗanda suka sami tikitin takara barazar ƙwace takarar ta su wasu kuma za a umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta da ta soke takararsu.

Yaa kuma bayyana wa magoya bayansa cewa, ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar ta APC (Raɗɗa) bai kira su ba don sulhunta tsakaninsu.

Haka nan, ya ce an sanar da shi Dikko Raɗɗa ya ƙi ɗaukar mutumin da aka ba shi shawarar ya ɗauka don yai masa mataimaki saboda mutumin ya goyi bayan shi (Inuwa) lokacin da aka gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

“Hakan ya nuna cewar ba ni kaɗai ba ne ba sa buƙata a jam’iyyar ba, har da magoya bayana ba a buƙatar su a tafiyar saboda haka ne muka sauya sheƙa,” inji shi.

Daga nan, Inuwa ya sha alwashin zai tabbatar Jam’iyyar PDP ta yi nasara a zaɓe mai zuwa a jihar.

“Ina tabbatar maku cewa tarihi zai maimaita kansa kamar yadda muka juya wa PDP baya a zaɓen shekarar 2015, a wannan karon za mu juya wa APC baya mu ƙi zaɓen su, kuma na tabbata PDP ce za tai nasara,” inji Inuwa.

A nasa ɓangaren, Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ya bayyana sauya sheƙar a matsayin cigaba a jam’iyyar, inda ya bayyana fatansa na ganin jam’iyyar ta yi nasara a zaɓen 2023 .

Ya zuwa haɗa wannan labari, Jam’iyyar APC ba ta ce uffan ba dangane da sauya sheƙar tsohon Sakataren gwamnatin jihar da ɗaruruwan magoya bayansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *