Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mutumin da ya yi wa Jam’iyyar PDP takara a zaɓen Gwamnan Jihar Ogun na 2023, Ladi Adebutu, a ranar Talata ya isa kotun sauraron kararrakin zaɓen jihar da shaidu har guda 8,000.
Ɗan takarar dai na ƙalubalantar nasarar da Dapo Abiodun ya samu a zaɓen Gwamnan Jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris ɗin da ya gabata.
A kwafin ƙarar tasa mai lamba EPT/OG/GOV/03/2023, ɗan takarar ya ce ya shigar da ƙarar ce saboda yana zargin ba a bi Dokar Zaɓe ta Nijeriya ba a yayin zaɓen.
Alqalai uku ne dai suke sauraron ƙarar, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamidu Kunaza suka ci gaba da sauraron ƙarar a ranar Talata.
Lauyan Ladi Adebutu, Goddy Uche (SAN) ne dai ya gabatar da shaidun waɗanda ke cikin jakukunan ‘Ghana mas go’, a gaban kotun wacce ke zama a Kotun Majistare da ke Isabo a Abeokuta, babban birnin jihar.
Ya roƙi kotun da ta karɓi hujjojin sannan ta yi amfani da su. Lauyan ya ce gabatar da shaidun ya biyo bayan buƙatar hakan da kotun ta yi daga vangarorin shari’ar guda biyu.
Goddy ya kuma ce ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da Gwamna Abiodun da jam’iyyar APC wani kundi mai shafi 98, wanda ke ɗauke da cikakkun dukkan hujjoji da shaidun da za su gabatar a gaban kotun.
Shaidun a cewarsa sun haɗa da wasu fom-fom na INEC da rahoton na’urar BVAS da fama faman ECA da rajistar masu zaɓe da kuma sakamakon da aka ɗora a shafin INEC na intanet.
Sai dai lauyan Gwamna Abiodun, Kehinde Ogunwunmiju, ya yi kira ga kotun da ta yi fatali da shaidun saboda ba su bi ƙa’idojin da ya kamata ba.
Daga nan ne Mai Shari’a Hamidu Kunaza ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa nan da ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.