Ɗan takarar gwamnan APC a Sakkwato na gab da lashe zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA

Ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu na gab da samun nasara bayan ya lashe ƙananan hukumomi 16 cikin 20 da aka ayyana kawo yanzu.

Sakkwato tana da ƙananan hukumomi 23.

Aliyu ne ke jagorantar ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar Ubandoma da ƙuri’u 41,585.

A sakamakon zaven, ɗan takarar APC ya samu ƙuri’u 352,606 yayin da Ubandoma ya samu ƙuri’u 311,021.

Ana ci gaba da jiran sakamakon sauran ƙananan hukumomi uku da suka rage.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *