Ɗan takarar Gwamnan Bauchi a APC Farouq Mustapha ya fice daga jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Bauchi a zaɓen 2023, Farouk Mustapha, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, Mustapha ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar ne bayan kayen da ya sha a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar.

Tsohon shugaban hafsan sojin sama, Sadiq Baba Abubakar ne dai ya lashe tikitin jam’iyyar mai mulki a zaɓen da aka yi na ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu.

Sai dai kuma, ɗan siyasar wanda ya ce ba za su zamo abokan gaba da yan tsohuwar jam’iyyarsa ba koda sun haɗu a ɓangaren adawa a zaɓe mai zuwa bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koma ba.

“Bayan dogon nazari da kuma shawara da ‘yan uwa da abokan hulɗar siyasa, na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC. “Ina matuƙar godiya ga shugabanni, da mambobin Jam’iyyar APC bisa ga dama da suka bani, na shiga jam’iyyar, har na yi takarar Gwamna a cikinta. Ba zan manta da wannan halarci ba.

“Na shiga Jam’iyyar APC ne domin bada gudunmawa wajen kawo cigaba a Jihar Bauchi! Sai dai ban samu daidaiton ƙudiri da shugabannin jam’iyyar ba. Hakan ya sa na yanke shawarar sauya sheƙa zuwa wani waje domin cigaba da gwagwarmaya don inganta rayuwar al’ummarmu.

“Ina neman alfarmar ‘ya’yan Jam’iyyar APC da su fahimce ni, domin ban ƙullaci kowa ba.

“Kuma duk da akwai yiwuwar mu kasance a ɓangarori masu hamayya da juna a lokacin zaɓe, hakan ba zai sa mu zama abokan gaba ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *