Ɗan takarar gwamnan NNPP a Katsina ya tsallake rijiya da baya

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP, Eng. Nura Khalil, ya tsallake rijiya da baya a hanyarsa ta zuwa Ƙaramar Hukumar Bakori inda zai kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jihohi da ke gudana.

Ɗan takarar ya ce ‘yan ta’adda ɗauke da makamai sun tare hanyar da tawagarsa za ta bi don zuwa mazaɓar tasa.

“Mun wuce Ƙanƙara daidai mararrabar Katikawa sai muka ga ana tsaida mu, muka tsaya sai ga wani mutum ya zo ‘yan ta’adda sun fasa masa kai,” Inji shi.

Ya ce wasu sun gaya masu cewar akwai ‘yan ta’adda a kan hanyar lamarin da ya tilasta suka sauya hanya.

Nura Khalil ya yi godiya ga Allah bisa tseratar da shi daga farmakin ‘yan ta’addar.

Daga bisani, ɗan takarar ya isa rumfar zaɓensa tare da mai ɗakinsa, Hajiya Farida, inda suka kaɗa ƙuri’arsu a mazaɓar Kandarawa cikin Ƙaramar Hukumar Bakori ta jihar.

Bayan kaɗa ƙuri’ar tasa, ɗan takarar ya bayyana cewar duk da wasu jam’iyyu a jihar na ba wa masu zaɓe kayan masarufi, suna hangen jam’iyyarsu ce da nasara saboda a cewarsa mutane, musamman mata na karɓar kayan da ake raba masu amma kuma suna zaɓar jam’iyyarsu mai alamar kayan marmari.