Ɗan takarar Gwamnan Ondo, Dokta Akintelure ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar gwamnan Jihar Ondo ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dr Paul Akintelure, ya kwanta dama.

An tabbatar da mutuwarsa ne da safiyar Talata, 26 ga Maris, 2024.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata marigayi Akintelure ya yi ƙorafi kan barazanar kisa da yake fuskanta.

Bayanai sun ce likitan da ya duba shi ya ce, Akintelure ya rasu ne a Legas.

Kafin wannan lokaci, mai magana da yawun marigayin, Oladapo Akintelure, ya faɗa a cikin wata sanarwa da ya fitar cewar yana da yaƙinin barazanar da ake yi wa maigin nasa zai gushe.

Sai dai ya nuna damuwa kan yadda lamarin ya tsananta tun bayan da aka ayyana ran 25 ga watan Afrilu, 2024, a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen fidda gwani a jihar.

Haka nan, ya ce ya kai rahoto ga hukumomin tsaron da suka dace, kana ya samu bayanan sirri da kuma shawarwari.

An ce kafin rasuwarsa, marigayi Akintelure na da kusanci da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.