Ɗan takarar Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya

Daga WAKILINMU

A jiya Lahadi ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya Masarautar Kwatarkwashi game da
rasuwar sarkin masarautar, Mai Martaba Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi.

Dauda Lawal wanda shi ne ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, ya kai ziyarar ne da zimmar jajanta wa masarautar da ma al’ummarta bisa wannan babban rashin.

Idan dai ba a manta ba, marigayi Mai Martaba Sarki Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi ya rasu ne a ranar Alhamis, 9 ga Yunin 2022.

Sabon sarkin masarautar, Mai martaba Alhaji Ahmad Garba Bunu ne ya amshi baƙuncin tawagar ta Gamjin Gusau wacce ta ƙunshi manyan makusanta da jiga-jigan tafiyar siyasarsa.

Bayan jajanta wa sabon sarki da masarautar, Dauda Lawal ya jajanta wa al’ummar Kwatarkwashi bisa wannan babban rashi da aka yi, inda ya bayyana kyawawan halaye na marigayi sarkin.

Ya ce: “ Marigayi Sarki dattijo ne mai dattako, kuma uba ne wanda ya tafiyar da al’ummarsa ba tare da nuna bambanci ba. Ba kawai a Kwatarkwashi ba, marigayin jigo ne a bakiɗaya Jihar Zamfara.

“Ina taya sabon sarki murna wannan ni’ima da Allah Ya yi mishi, sannan kuma ina addu’ar Allah Ya ba shi ikon gudanar da mulki cikin hikima. Allah Ya kyautata makwancin marigayi, Ya kai haske kabarinshi.” In ji shi.