Ɗan takarar PDP ya doke ƙanin Abdulsalami Abubakar a Neja

Daga WAKILINMU

Ɗan takarar Majalisar Wakilai na PDP a shiyyar Chanchaga a jihar Neja, Abubakar Abdul Buba, ya doke takwaransa na APC Abubakar Adamu wanda ƙani ne ga tsohon Shugaban Ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar.

Da take bayyana sakamakon zaɓe a Minna babban jihar, baturiyar zaɓen, Farfesa Mercy Modupe Adeyeye, ta ce Buba (PDP) ya samu ƙuri’u 35,688, yayin Ado Salami (APC) ya tsira da ƙuri’u 19, 282.

Ta ce ɗan takarar NNPP, Ibrahim Abdulaziz, ya samu ƙuri’u 1,747, sannan ɗan takarar APGA, Usman Musa Ndakpayi, ya samu 2,548, yayin da Abdullahi Musa na jam’iyyar Labour ta ƙare da ƙuri’u 2, 875.