Daga RABIU SANUSI
Bayanai daga Jihar Zamfara na bayyana cewa ɗan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma sanatan ɗaya daga shiyyoyin jihar, Ahmad Sani Muhammad Yariman Bakura, ya lashe zaɓen kujerar Majalisar Tarayya ƙarƙashin mazaɓun Bakura da Maradun.
Hon Ahmad Sani Muhammad Bakura ya samu wannan nasarar ne da ƙuri’a 55,273 inda ya doke abokin takarar sa Muhammad Bakura Ahmed wanda ya samu kimanin ƙuri’a 17,559
Sakamakon Wanda baturen zaɓe na mazaɓar, wato Dr. Ahmad Kainuwa na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau ya bayyana a hedikwatar tattara sakamakon zaben dake Maradun.
Ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ɗakin tattara sakamakon Abubakar Jafar Maradun ya ce bayyana sakamakon zaɓen ya tabbatar da cika alƙawarin da suka ɗauka yayin da jama’a ke kira wajen ya kamata ya fito ya jaraba kuma za su zaɓe shi.
Yayin da yake taya murna ga sabon ɗan Majalisar Tarayyar na Bakura/Maradun, ya ce ya fatan zai yi matuƙar ƙoƙari wajen ganin ya yi aiki ga al’ummar sa ba tare da gajiyawa ba.