Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa, gudunmawar da kamfanin Dangote ke bayarwa ga tattalin arzikin Nijeriya na da matuƙar muhimmanci kuma ba a taɓa yin irinsa ba.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a wajen taron haɗin gwiwa karo na 52 na ƙungiyar Masana’antun Nijeriya (MAN) a jihar Kano.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Hon. Adamu Aliyu Kibiya, ya ce, an kuma bayyana ƙungiyar ta Afirka a matsayin babbar cibiyar ƙwadago a kamfanoni masu zaman kansu.
Kamfanin Dangote na ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin gudanar da harkokin MAN na 2024 da aka kammala a jihar Kano.
Ya ce, ta hanyar saka hannun jari da dama da ƙoƙarinsa na samar da arziki, tattalin arzikin Nijeriya yana bunƙasa.
Gwamna Yusuf wanda ya ziyarci rumfar kamfanin, inda ya ce shirye-shiryen sa na taimakon jama’a sun yi tasiri sosai.
A cewarsa, matatar Dangote kaɗai na da ƙarfin da za ta iya magance matsalar canjin kuɗacen ƙasashen waje ta Nijeriya ta hanyar rage yawan buƙatu na shigo da man fetur daga aasashen waje.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar MAN Bompai da reshen Jigawa Alhaji Mohammed Bello Isyaku Umar ya bayyana cewa ƙungiyar na alfahari da irin nasarorin da kamfanin Dangote ke samu da kuma ɗimbin jarin zamantakewa.
Da yake tabbatar da Gwamna Yusuf, a kwanan baya, wani rahoto ya bayyana cewa matatar mai ta Dangote na da ƙarfin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan zuwa dala biliyan 322 nan da shekarar 2025.
Rahoton mai suna ‘Tasirin Matatar Dangote Ga Tattalin Arzikin Nijeriya’, wanda Kamfanin Data Serɓices & Resources ya fitar, a sanadiyyar matatar, ana sa ran tattalin arzikin Nijeriya zai ƙaru da kashi 3.34 cikin 100 a shekarar 2024, inda zai ƙaru zuwa kashi 4.13 bisa 100 zuwa 2030.
An yi hasashen cewa, a yayin da matatar ta ke aiki, ana hasashen ƙaruwar tattalin arziki zuwa kashi 4.15 cikin 100 a shekarar 2024, zai kuma kai kashi 6.21 cikin 100 nan da shekarar 2030.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, tattalin arzikin Nijeriya a farashin kasuwan yanzu zai ƙaru daga Naira Tiriliyan 234.43 a shekarar 2023 zuwa tiriliyan N304.8 a shekarar 2024, tare da ƙarin girma zuwa tiriliyan N364.94 a shekarar 2025.
Ya ƙara da cewa, nan da shekarar 2026, ana hasashen tattalin arzikin Nijeriya zai kai Naira Tiriliyan 432.24, inda zai haura tiriliyan N806.91 nan da shekarar 2030.