Ɗangote na neman rancen Naira biliyan 638 kafin 2023

Daga AMINA YUSUF ALI

Mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote yana buƙatar rancen Naira biliyan 638 don ƙarasa ginin matatar man wacce yake so ya kammala kafin nan kafin shekarar 2023. Kamar yadda jaridar Ingilishi ta News Business News ta rawaito. 

A wani sakamakon rahoto da kamfanin Fitch wanda ya yi fice wajen bincike a Duniya ya yi hasashen cewa, mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Ɗangote dole zai buƙaci rancen Naira biliyan 638 don kammala matatar man da ya fara ginawa wacce ake sa ran za ta lamushe har Dalar Amurka biliyan 19. 

Alhaji Dangote ya yi alƙawarin kammala matatar man har ta fara aiki kafin ƙarshen zangon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, wato shekara mai zuwa. 

Kamfanin Fitch ya bayyana cewa, ana sa ran matatar za ta fara aiki ne a tsakiyar shekarar 2023 wato kusan lokacin ajiye mulkin Buhari kenan. 

Ya ƙara da cewa, samun kammala kamfanin da wuri ko jinkirinsa ya ta’allaƙa ne ga samun jarin da Ɗangote ya yi. Domin a halin yanzu Ɗangote ba shi da irin wannan kuɗin da zai iya kammala wannan gagarumin aikin kafin shekarar 2023.

A cewarsu, a yanzu abinda biloniyan attajirin yake nema shi ne, ƙarin Dalar Amurka biliyan $1.1. Domin ya riga ya zuba kuɗaɗensu sosai har ma ya yi rance da yawa duk ya zuba a cikin ginin matatar. 

Wato kenan, ana nufin a cikin shekarar nan Ɗangote yake son kuɗin ya kammala matatar wacce ake sa ran a shekara mai zuwa za ta fara aiki.