Ɗangote zai haɗe kamfanoninsa na gishiri, shinkafa da kuma na sukari a waje guda

Daga AMINA YUSUF ALI

NASCON kamfanin samar da gishiri a ƙarƙashin rukunin kamfanonin Ɗangote yana shawarar haɗewa tare da wasu kamfanonin abinci guda biyu daga cikin rukunin kamfanonin nasu. Wato kamfanin shinkafa da na sukarin Ɗangote.

Za a tattauna a kan wannan al’amari a samar masa matsaya a taron kwamitin daraktocin kamfanonin da za a gudanar nan gaba a cikin wannnan watan.

Wannan haɗaka da ake sa ran yi tana zuwa ne watanni 31 bayan babban kamfanin da yake hamayya da kamfanin Ɗangoten, BUA Group, ya ba da sanarwar yin wannann haɗaka ta haɗe kamfanoninsa na shinkafa, sukari, fulawa, man girki, da fulawa zuwa kamfani ɗaya tilo mai suna BUA Foods.

BUA Foods a halin yanzu dai shi ne mafi girman kamfanin sayar da kayan masarufi na Nijeriya wanda ƙarfin arzikinsa ya kai sama da Naira tiriliyan 2.4.

BUA Group mallakin Abdul Samad Rabiu ne, mutum na biyu ma fi arziki a Nijeriya kuma mutum na huɗu mafi arziki a Afirka.

Ƙarfin arzikin kamfanonin Sukari Ɗangote da NASCON sun buxe kasuwanci ranar Alhamis a kan Naira biliyan 329.8 da Naira biliyan 70.2.

Kuma kamfanonin biyu suna da ƙarfin darajar kadarorin da suka kai Naira biliyan 558.9 da Naira biliyan 59.2 a qarshen watan Maris ɗin da ya gabata.

Haka shi ma kamfanin BUA Group kamar yadda Ɗangote ya gina matatar mai da ta lamushe Dalar Amurka biliyan 19, yana shirin gina matatar mai a jihar Akwa Ibom da zai dinga samar da gangar mai 200,000 a kowacce rana. Ana sa ran zai zo nan da shekarar 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *