Ɗanwaire gwanki sha bara (1924)

Daga FATUHU MUSTAPHA

Babu takamaiman ko wacce shekara aka haifi Ɗanwaire, sai dai an bayyana cewa asalin sunan sa Muhammadu. Iyayen sa da alama dai Fulani ne, kuma asalain sa shi da mutumin Kano ne. an haife shi a garin Waire da ke ƙasar Bichi a yanzu. Babu kuma wani cikakken bayani akan ko wane irin nau’in Fulani ne. A taƙaice dai, asali da tasowar Ɗanwaire abu ne da har yau masana basu samu wani cikakken bayani a ka ba. Amma dai an fara jin ɗuriyar Ɗanwaire ne a zamanin sarkin Kano Bello1882 – 1893. Hakan na nuni da cewa da alama an haifi Ɗanwaire tun a cikin shekarun 1850.

Tarihi ya fara jin labarin Ɗanwaire tun bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin Sarkin Kano bello da Sarkin Gumel Habu Nakata. Koda yake bawani cikakken musabbabin yaƙin in banda ‘yan tsegunguma da suka shiga tsakani, da kuma ƙoƙarin da shi sarkin Gumel habu ya yi na ya kame Ɓaɓura. Wannan dai shi ne za a iya cewa abinda ya janyo rikicin.

Domin a wata wasiƙa da Bello ya aikewa Sarkin Musulmi Abdu Ɗanyen Kasko ya bayyana masa yadda Sarkin Gumel ɗin ya sanya dakarun sa suka yi wa Ribaɗin na Ɓaɓura ƙawanya har tsawon kwanaki. Wannan rikici shi ya fara ƙamari a tsakanin masarautun biyu da har ta sanya, kowanne ya ɗauki aniyar fito na fito da xan’uwan sa.

To amma shi Bello baya zuwa yaƙi, dan haka sai ya nemi wanda zai biya ya tarar masa Sarkin Gumel, a sabili da haka aka ɗauko masa sojan haya, wato Ɗanwaire. Shi kuma nasa ɓangaren jin ga wanda aka ɗauko, ya sanya ya fara neman yadda zai ƙarawa daɓen sa makuba.

Musamman ma a lurar da ya yi na cewa mayaƙan sa sun tsorata da jin labarin da Ɗanwaireb za su kara. Dan haka shi ma sai ya nemo Ɗanfurya, wanda a lokacin rikicin Rabe a Borno ya sanya ya yi ƙaura zuwa Kafin Hausa. Yadda da Ɗanfurya ya yi na ya shiga tawagar sarkin Gumel Habu ta sanya a wannan fitar ma bai nemi Ɓaɓura ba, sai ya dosa kano. Sai dai tun a wannan lokaci, Ɗanwaire ya kafa sansani a Kanyar Maiƙaho.

Sarkin Gumel ya fito cike da mayaƙa, da kuma masarta suna zuga shi, suna “Sarkin Gumel Habu Nakata, wanda bai san ba gates, a garin na gates anan ya san na biki”. Har ya iso Kanyar Maiƙaho bai san Ɗanwaire na nan na dakon su ba. Ko hutawa ba su yi ba, ya far musu da yaƙi, in ya keto su daga farko sai ya dire zuwa ƙarshen su, sai ya yi musu baduhu ya ɓace, sai dai su kuma jin sa ya faɗo su ta Kudu. Wannan salo da Ɗanwaire ya gwada musu ya firgita su ainun. Ba dan Ɗanfurya yana cikin su ba, da ya tonawa Gumulawa asiri a ranar. Ganin haka ya sanya, Sarkin Gumel ya bayar da izinin a koma gida a sake shiri.

To amma kafin ya sake shirin, tuni Damagarawa sun sha masa kai, dan haka ya manta da yaqin Kano, ya maida himma kan fitinar Damagarawa da ke neman su tarwatsa masa ƙasa.
Wannan nasara da Ɗanwaire ya yi, ta janyo masa farin jini an idon Bello, inda har ya naɗa shi Sarkin Fulanin Bichi. To amma bisa ga dukkan alamu, Ɗanwaire ya yi samun fadar wawa, da ya samu fada ya zagi uwar sarki, kamar dai yadda zamu gani nan gaba.

Wannan abu ya faru ne, bayan Sarkin Musulmi Abdurrahman ya umarci dukkan sarakunan Fulani da su aike da tawaga domin ya yaƙi Argungu, musamman na ya cika burin sa na ya kama Sarkin Argungu Sama ɗan Nabame.

A wannan lokaci Sarkin Kano Bello ya tura da tawagar Kano ƙarƙashin Galadiman Kano, kuma babban ɗan sa Muhammadu Tukur, kuma har da Ɗanwaire a wannan tawaga. Suna zuwa suka faɗa yaƙi, kuma ana cikin yaƙin ne sai aka harbi dokin Ɗanwaire. Da Ɗanwaire ya waiga sai ya ga Tukur a bayan sa, dan haka ya doshe shi ya ce masa “maza sauka ka bani dokin ka.”

Wannan magana ta yi wa Tukur ciwo, ya wani bara zai kalli ɗan sarki kamar sa, kuma Galadiman Kano ya ce masa ya sauka ya ba shi doki!! Wani abin da ya 2arawa Tukur vacin rai shi ne yana kallon wai waye Ɗanwaire a fagen daga da har ya isa ma ya tunkare shi? Ganin yadda ran Tukur ya vaci, ya tabbatar da cewa, yadda Bello ya ƙallafa Tukur a ran sa, matukar ya koma Kano to fa kashin sa ya bushe. A wannan lokaci ya buɗe wani sabon babi a rayuwar sa. Don haka tun a nan ya kai caffa ga Sarkin Katsina.
Zuwan Ɗanwaire Katsina abin nan aka yi da ake cewa, Yaro na murna ya samu doki, doki na murna ya samu yaro.

Domin kuwa a lokacin da Sarkin Katsina ke murnar samun mayaƙi kamar Ɗanwaire, shi kuma Ɗanwaire murna ya ke ya samu sabuwar mafaka, inda zai zauna ya shaƙata ya miƙe ƙafafun sa. A wannan lokaci Katsina na fuskantar matsin lamba daga Ɗanbaskore a Tasawa, Sarkin Gobir Almu da kuma Ƙaura Hassan a Maraɗi. Kowanne kuwa abin tsoro ne a fagen daga, ga shi kuma a wannan lokaci Durɓin Katsina Dikko ne kawai ke iya juyar da su in sun tasowa Katsina. Dan haka zuwa Ɗanwaire Katsina ba ɗaramar sa’a a ka taka ba. Nan da nan Sarkin Katsina ya yi maraba da shi, ya kuma ba shi izinin ya kafa ribaɗi a Ruma.

Babban dalilin kafa wannan ribaɗi shi ne, dan ya hana Sarkin Gobir Alamu sakat, wato dai yanzu Durɓi na tsare Arewa maso Gabas, shi kuma Ɗanwaire na tsare Arewa maso Yamma. Waɗannan bayin Allah biyu su suka sanya katsina ta zama kamar garwashin wuta a wurin Maraɗawa da Gobirawa. Dalilin da ya sanya Ɗanbaskore ya bar Maraɗi ya koma Tasawa, sa’annan ya canja salon yaƙin sa ya dai na kai yaƙi sai dai ya kai hari da wata ‘yar ƙaramar runduna.

Ɗanwaire a cewar sarkin Katsina Dikko, mutum ne da baya da ragawa a fagen yaƙi, ga tsiwa in dai ya shiga fagen daga. An haƙƙaƙe mutum ne da baya tsoro, domin haka ma ya zama kai kaɗai gayya. Komai yawan tawagar yaƙi Ɗanwaire baya shayin ya tunkare ta balle har ta razana shi. Gogagge ne a fagen yaƙi na aje a gayawa sarki. Zuwan sa shi ya canja akalar masu gaba da Katsina, suka fara razana suka daina gaba da gaba da mayaƙan Katsina. Yayi iya yin sa, har ya zamanto a wannan lokaci in ance Dikko to sai ace Ɗanwwaire sannan a shafa fatiha, in dai batun yaƙi ne.

Bayan da Turawa suka ci Katsina da yaƙi, sai ya ci gaba da zaman sa a Ruma. To amma da aka naxa Dikko ya zama sarki a katsina, sai kuma rikici ya shiga tsakanin su, musamman raini da ya shiga tsakanin Sarkin Dikko da Ɗanwaire. Ance yana cikin hakiman da suka ƙi yadda su yi wa Dikko mubayi’a. Dan haka sai Dikko ya kwaɓe shi, inda shi kuma ya ke ganin waye wani Dikko da zai kwaɓe shi. Har sai da takai Turawa sun sanya an kama shi an kai shi fursun. Sai dai ba a fi shekara ba aka sake shi aka kuma maida shi sarautar sa ta Ruma.

Allah ya yi wa Ɗanwaire rasuwa a shekarar 1924, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Har ana zaton ko hannu aka sa masa. A yanzu haka zuriyar sa ke riƙe da ikon ƙasar Ruma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *