Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ranar Litinin ne wani rahoto da Bloomberg ta wallafa a shafinta na Bloomberg ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya na shirin miƙa gangar ɗanyen man Nijeriya har 400,000 a kowace rana ga matatar Dangote.
Ta ce ana sa ran wannan gagarumin ci gaba zai faru nan da watanni biyu masu zuwa, wanda ya kai ganga miliyan 24 na wadata Nijeriya tsakanin Oktoba da Nuwamba 2024.
Wannan haɓakar zai iya yin tasiri mai muhimmanci ga ayyukan matatar da kuma masana’antar mai na cikin gida, kuam zai sauya tsarin kasuwannin shigo da kayayyaki na yankin.
Wannan sabon lamari ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na cewa an fara cinikin ɗanyen mai a naira.
A ranar Litinin ne dai aka samu labarin cewa Kamfanin Mai na Nijeriya ya shirya fara samar da ɗanyen mai a cikin Naira ga matatar man Dangote a wannan makon tare da wasu matatun mai guda uku da za su fara samar da man fetur.