.Shugaban kamfanin NNPCL , malam Mele Kyari ya rasa ‘yarsa Fatima wadda ke da shekaru 25 a duniya a ranar Juma’a.
Sai dai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jajanta wa Kyari da iyalansa, inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙan Fatima da rahama.
Shettima ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa ‘yan uwa hakurin jure wannan babban rashi.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bi sahun sauran masu jana’iza, wanda aka gudanar a masallacin Annur da ke Abuja.