Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa, matsalar ɗumamar yanayi na barazana ga matalautan ƙasashe, wanda idan har ba a ɗauki matakan gaggawa ba, za ta fara haifar da hasarar rayuka nan da shekarar 2060.
IMF ya ce, za a samu ƙaruwar kaso 8.5 na adadin rayukan da za a yi asara, musamman a yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi, kuma kaso 14 na waɗannan ƙasashe za su fuskanci qaruwar tsananin zafi.
Daga cikin ƙasashe 39, wanɗanda ke ɗauke da kusan mutane biliyan guda na al’ummar duniya, rabi daga cikinsu da ke fama da wannan matsala sun fito ne daga nahiyar Afirka.
Sama da mutum miliyan 50 ne a waɗannan ƙsashe za su fuskanci tsananin yunwa a 2060, saboda ƙalubalen da ka iya dabaibaye hanyoyin samar da abinci da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Hakan ta sanya IMF kira ga shugabannin ƙasashen duniya da za su gudanar da taro kan matsalar ɗumamar yanayin a Ƙasar Kenya, domin samo mafita, musamman ga matalautan ƙasashe.
IMF ya ce nan da shekarar 2040, waɗannan ƙasashe za su iya fuskantar yanayin zafi sama da digiri 35 a ma’aunin celcius kwatankwacin na kwanaki 61 a shekara fiye da sauran ƙasashe.