Ƙagaggen rubutu tamkar ɗa ne wajen mahaifinsa Adabi, shi ko adabi daji ne ba a yi masa ƙyaure- Khalid Imam

Waka saƙa ta ake yi kamar tabarmar kaba, shi kuma zube gina shi ake kamar yadda ake gida – Khalid

Daga AISHA ASAS

Shahararre kuma sanannen marubuci da ake alfahari da shi a duniyar Adabin Hausa Khalid Imam, ya samu damar amsa gayyatar jaridar Manhaja inda masu karatu za su ji cikaken tarihi tare da nasarorin da ya samu a duniyar rubutu. An dai ce waƙa a bakin mai ita za ta fi zaƙi, ku biyo mu don jin wane ne Khalid Imam:

Masu karatu za su so jin tarihin ka.
Suna na Khalid lmam. An haife ni a shekarar 1973 a Unguwar Yakasai da ke cikin Birnin Kano. Ni marubuci ne wanda aka buga wasu daga rubuce-rubuce na a littattafai da muƙalun ilimi a ƙasashen duniya kamar su Amurka da Jamus da Indiya da ƙasar Poland da kuma ƙasar Nepal. Ni mutum ne mai matuƙar sha’awar harkar koyarwa kasancewa ta malamin makaranta na sakandare. Ina da sha’awa sosai a fagen bincike-bincike da kuma rubuce-rubuce. An buga wasu da yawa daga rubuce-rubuce na kamar waƙoƙi ko sharhi a jaridu da mujallu da ke gida Nijeriya na Turanci da na Hausa masu yawa.

Kasancewa ta marubuci na taɓa zama mataimakin shugaban ƙungiyar marubuta ta Nijeriya reshen jihar Kano wato (Association of Nigerian Authors, Kano State Branch). Haka kuma ni ne na kafa kuma na zama shugaban ƙungiyar Dandalin Sha’irai (All Poets Network). A cikin watan Satumba na 2017, na samu halartar wani shiri na musamman a ƙasar Lebanon wanda Jami’ar ‘Notre Dame’ da Gidauniyar ‘Cedars’ duk na ƙasar Lebanon tare da haɗin gwiwar Gidauniyar ‘Wole Soyinka’ ta ƙasar Nijeriya su ka shirya wa zaƙaƙuran marubuta goma ‘yan asalin Nijeriya don nazarin tarihin duniya da al’ada da adabi da addini. Shi wannan shirin bita na SAIL wato (Study Aboard in Lebanon) ana shirya shi ne da fatan ya ƙara danƙon zumunci tsakanin dukkan ƙasashen da marubutan ta su ka amfana da shirin da kuma ita ƙasar Lebanon.

A halin yanzu ni ne Shugaban Kamfanin ‘Whetstone Arts & Translation Services’ kuma Babban Daraktan Makarantar Khalid Imam Academy wadda mu ke bai wa marayu damar yin ilimi mai inganci a kyauta. Kasancewar ina da sha’awa da kuma ƙwarewa a fagen aikin fassara, haka ta sanya nakan yi aikin fassara ga hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kan su na ƙasa-da-ƙasa kamar su ‘Clinton Health Access Initiatives’ (CHAI) da ‘Mobilising for Development’ (M4D) da Mafita da ke ƙarƙashin Adams Smith. Na zama editan mujallu da dama musamman waɗanda ake wallafawa a cikin harshen Turanci. A halin yanzu ni ne editan shafukan adabi na mujallar Turanci ta wata-wata mai suna Platform. Haka kuma ni nake rubuta shafin nan mai suna Sirrin Arziki da Nasara a Mujallar Muryar Arewa wanda ta ke fita a wata-wata.

Na sha karɓar lambobin yabo daga jaridu da hukumomi da ƙungiyoyi masu yawa na gida da wajen Nijeriya kamar su Inuwar Jama’ar Kano da STSB da ANA Kano da PIN da ELTAK. Ina da aure kuma Allah Ya azurta ni da ‘ya’ya maza guda huɗu ga su kamar haka: Khalid (Alhaji) da Shu’aib (Abu Madayyana) da Ahmad da kuma Jamilu.

Ka kasance marubucin waƙa ne kawai ko ka na taɓa wani ɓangare da ba waƙa ba?
A’a, a gaskiya kamar yadda na fara bayyanawa a baya, ni ba marubucin waƙa ba ne kawai. A fagen Adabi, zan iya cewa ba ni da gefe duk da cewa wasu sun fi sani na da rubuta wasan kwaikwayo da waƙe, wanda sanadiyyar hakan ne na taɓa zama zakara a fagen gasar rubuta wasan kwaikwayo har sau biyu. A shekarar 2009 na yi nasarar lashe kyautar Tagulla a gasar ƙasa ta rubutun wasan kwaikwayo cikin harshen Hausa da aka shirya don tunawa da marigayi Injiniya Bashir Ƙaraye a can Birnin Tarayya Abuja. Kazalika, a shekarar 2010 na sake lashe kyautar Zinare a Gasar Jiha ta Rubutun Wasan Kwaikwayo Cikin Harshen Turanci wanda Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gudanar don tunawa da Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya.

A fagen rubutun waƙe kuwa, a shekarar 2013 na yi bajintar zama Musulmi ɗan Arewa kuma Bahaushe na farko da ya shiga cikin mashahuran zakaru uku na Gasar ƙasa-da-ƙasa da aka fi sani da Korea-Nigeria Poetry Feast ta hanyar lashe kyautar Tagulla a Gasar Shekara-Shekara a fagen Rubutun Waƙe da harshen Turanci. Har ila yau, a watan Maris na shekarar 2015 na sake samun nasarar zama ɗaya daga cikin mashahuran masu rubuta waƙe da harshen Turancin da aka sake karramawa a wajen wannan gasa ta ƙasa-da-ƙasa ta Korea-Nigeria Poetry Feast da ake yi duk shekara a Birnin Tarayya Abuja.

Wace shekara ka fara rubutu?
Tan! Ai kam dai zan iya cewa na fara rubutu ne tun ina ɗalibi a COE Minna amma dai na fi zaton an fara buga rubutuna ne a jaridar Weekly Trust a shafinsu na Adabi wanda Ibrahim Sheme ya ke gudanarwa a lokacin a cikin shekarar 1999. Na kuma fara buga littattafai wanda na tattara waƙoƙin ɗalibai na da nake koyawa rubutu a makarantar GTC Ungogo wanda na zama editan sa a shekarar 2004 wato A ‘Citadel of Excellence’ da kuma ‘A Bird’s Evidence’ shi kuma a shekarar 2005. Sai kuma na wallafa littafina na wasan kwaikwayo wato ‘Sodangi’ a shekarar 2009. Sai a shekarar 2010 da na wallafa littattafai biyu da na waƙoƙin Turanci na yabo da nai wa marigayi Sarkin Kano Ado Bayero mai suna ‘The Song of San Kano’ da kuma ‘Letter to my Students’.

Kana ɗaya daga cikin editocin littafin waƙoƙi kan Annobar Korona mai suna “Corona Blues”, faɗa wa masu karatu yadda littafin ya samo asali?
‘Littafin Corona Blues’ shi ne kundi na farko da aka taskace waƙoƙi da mashahuran marubuta waƙoƙi cikin harsunan Hausa da Turanci suka taru suka rubuta a Nijeriya. Littafin ƙungiyar ‘All Poets Network’ ce ta yi ƙoƙarin tattara su da buga su tare da tallafin wata ƙungiyar tallafawa ci gaban al’umma da ke a Kano mai suna CITAD tare da tallafin Gidauniyar ‘MacArthur’ da kuma Cibiyar Tallafawa Ilimi ta Duniya wato ‘International Institute of Education’. Littafin ya samu karɓuwa sosai domin har an gudanar da taro na duniya a kan sa a dandalin Zoom wanda Cibiyar Ilimin Kimiyya ta Ƙasar Poland wato ‘Polish Academy of Science’ ta shirya cikin farkon watann Afrilu, 2021. Masana daga ƙasashen Jamus da Birtaniya da Amurika da Daular Larabawa da Ghana su ka halarta.

Wasu marubuta rubutacciyar waƙa da yawa na ganin duk waƙar da ba ta da ƙafiya ba ta cika waƙa ba. A nazari na ilimi ya zancen ya ke?
Babu shakka, ƙafiya ɗaya ce daga cikin manyan tubalan gina waƙa ko turakun dubawa a fagen nazarin rubutacciyar waƙar Hausa kamar yadda wasu masana da manazarta su ke faɗi ba don komai ba sai don ta na ƙara wa waƙa zaƙi wajen rerawa da saurare ko yi mata kwalliya sosai. Amma inda gizo ya ke saƙar shi ne ita ƙafiya kayan aro ce. Ba ɓoyayyen lamari ba ne cewa Bahaushe ya aro yin amfani da ƙafiya ne daga sigar yadda Larabawa su ke ginin baitocin waƙoƙin su. Cewa waƙa ba ta cika ba sai in har an yi mata ƙafiya a fagen nazari a ilmance ba komai ba ne illa shaci-faɗi. Tabbas babu wani masani ko guda ɗaya da ya taɓa faɗin cewa tilas ne yin waƙa da ƙafiya. Ra’ayi ne kawai na wasu masana cewar waƙa in ba ta da ƙafiya kamar wai ta na da rauni, amma sam ba gaskiya ba ne, wannan ya sanya a fagen nazari a ilmance ake da waƙa da ake kiranta da suna Ballagaza. A fahimtata yin waƙa da ƙafiya zaɓin marubuci ne abin da ake cewa shan koko ɗaukar wa rai.

Shin haka abin ya ke a mahangar marubuta ko ya abin ya ke?
Marubuci mutum ne wanda rubutu ya ba shi cikkakken ‘yanci da dama. Shi ƙagaggen rubutu kowanne nau’i tamkar ɗa ne wajen mahaifinsa Adabi. Shi ko adabi daji ne ba a yi masa ƙyaure a rufe garam. Wani ko wasu ba sa kallafa wa marubuci ƙa’ida wacce tilas wai sai ya bi sannan zai rubutu. Akwai bambanci tsakanin wannan shi ne tsari yadda ake rubuta kaza da kuma cewa wannan ƙa’ida ce tilas sai da ita rubutu kaza ya yi zai zama karɓaɓɓe. Kamar yadda aka sani adabi fage ne na aiki da basira don yin ƙirƙira, shi kuma aikin ƙirƙira ya na bai wa mai basirar yin sa wata irin cikakkiyar dama ta zama ‘yantacce a lokacin da ya ke gudanar da aikin ƙirƙirar sa. Shimfiɗa wa marubuci wasu sharuɗa a ce tilas sai ya bi su, kamar ƙoƙari ne na takure masa basira. Alal misali, marubuta kamar masu gina tukunyar ƙasa ne za su iya gina ta duk ta irin sigogi da suka ga dama matuƙar dai a ƙarshe sun samar da tukunya. Haka kuma suna da ‘yancin yi wa tukunyar duk irin adon da su ka ga zai fi ƙawata ta ba tare da sai wani ya yi musu tilas ba. Aikin marubuci ya sha bamban da na manazarci wanda sau tari shi akan ɗora shi ne bisa wani tsari don gudanar da aikin binciken sa. Marubuci ya na lura da tsari na duk yadda kowanne nau’i ko sigar rubutun kowanne fage ya ke amma wannan ba ta hana shi haifar da wata sabuwar siga idan ya na da sha’awar yin haka tunda dama aikin sa shi ne ƙirƙira. Cewa tilas ne waƙa ba za ta cika ba sai ta na da ƙafiya kamar mutum ya ce tilas ne sai da ludayi kawai za a dama fura. Kowa ya sani cewa tsari ne cewa sai an dama ake samar da fura da nono, amma ba tilas ba ne cewa damawar sai da ludayi kaɗai domin ana iya damawa da hannu ko a zamanance a dama da na’urar bilanda da dai sauran su. A gaskiyar magana cewa waƙa rubutacciya ba ta cika sai da ƙafiya kamar cewa ba za a sha fura da nono ba tilas sai da suga. Kowa ya san cewa shan fura da suga shan koko ne ɗaukar wa rai.

Tsakanin rubutun zube da na waƙa wanne ne ya fi wuya?
A gaskiya tsakanin rubutun zube da na waƙa zan iya cewa kowanne ya na da irin nasa ƙalubalen ko wuya, kuma ya danganta da buƙata ko bincike ko yanayi ko irin nishaɗin da marubuci ya ke ciki a lokacin rubutawa kowanne. Wani labarin na zube ya na buƙatar dogon bincike haka ita ma waƙar. Ya na da kyau mu lura cewa ita waƙa saƙa ta ake yi kamar tabarmar kaba, shi kuma zube gina shi ake kamar yadda ake gida. Kowanne ya na da irin tasa wahalar, amma dai abin da ya ke a bayyane shi ne ba kowanne marubuci ne ya ke iya rubuta waƙa ba, duk da cewa ba duk mai rubuta waƙa ba ne ya ke da basirar ƙagar rubutaccen labari. Ni a waje na a da can waƙa ta fi ba ni wahalar rubutawa, amma a yanzu da na mayar da hankali sosai a wajen rubuta ta zan iya cewa ta fi zube sauƙi da saurin rubutawa, domin in ta zo kamar shan ruwa ta ke a waje na.

Wasu na ganin cewa marubuta a wannan zamanin suna cin karen su ba babbaka, wanda ake ganin ya haifar da yawaitar littattafai marasa ma’ana, shin laifin waye?

Cin karen su ba babbaka kamar ya ya? Ban gane ba! In na fahimci tambayar so ki ke ki ce marubutan yanzu littattafansu ba su kai na marubutan da can inganci ba, in haka ne ai hakan ba wani mamaki domin damar da marubutan da su ka samu na yanzu ba su da ita. A lokacin su marigayi Abubakar Imam akwai kamfanoni masu yin ɗab’i kuma suna da editoci masu tace labari da gyaran duk wasu kura-kurai kafin a kai ga wallafa littafi ya shiga hannun masu karatu, shin yanzu akwai irin wannan damar? Ina Maɗabi’u irin su NNPC a yau ko makamantan su? Marubuci a da rubutun kawai zai yi ya miƙa a wani lokacin ma sa shi za a yi ana kuma yi masa zagi ta hanyar nuna masa yadda zai rubuta littafin ya ƙayatar, shin yanzu marubuta suna samun irin wannan gatan? Ashe kenan daga buhu sai tukunya da ke ganin wasu marubutan su na yi ba laifin su ba ne su kaɗai, rauni ne da yadda al’amura suka koma. Duk da cewa a yanzu ana samun cigaba marubuta su na sake fahimtar cewa aikin rubuta littafi ba na mutum shi kaɗai ba ne, akwai buƙatar editoci su duba su tace sannan akwai buƙatar sauraren shawarwari daga masana da manazarta don a haifar da littafi da zai zama zakaran gwajin dafi.

Waɗanne abubuwa ne marubucin waƙa ya kamata ya lura da su ko ya ba su muhimmanci a duk lokacin da ya ke rubuta waƙa?
Abubuwan da marubucin waƙa ya kamata ya lura da su ko ya ba su muhimmanci a duk lokacin da ya ke rubuta waƙa a gaskiya su na da yawa sosai. Tabbas muhimmin abin lura ne mai rubuta waƙa ya tabbatar waƙar sa ta na da baitoci da ɗango da jigo (wato ta na da saƙo ko saƙonni) da ma’auni da murya da sauran su. Salon rerawa da kari da rauji muhimman abubuwan lura ne a yayin rera waƙa da dai sauran su.

Me ya sa marubutan baya suka fi daraja a idanun mutane fiye da na yanzu?
Gaskiya sun fi mutunta al’adun Hausa a cikin rubutun su. Marubutan can shekarun suna fin daraja ne a idanun mutane masu shekaru fiye da matasan yau su ba sa ƙare basirar su wajen kwaikwayon al’adun Turawa ko Indiyawa a cikin rubutun su, ko da ma za su yi aro ne sukan baddala labarin da su ka aro ne su mayar da shi ya yi daidai da al’adu da rayuwar Hausawa. Labarun da su ke cikin littafin Magana Jari Ce na marigayi Abubakar Imam babu wanda zai karanta su ya ce asalin su daga labaran Turawa ne ko na Larabawa da Turkawa saboda salon da marubucin ya bi wajen Hausantar da su. Wasu marubutan kuwa na yanzu a wajen su kwaikwayon baƙin al’adu da sunan zamani a wajen su shi ne burgewa da nuna su wai masu ilimi ne da wayewa saboda shagalta da ruɗuwa da kuma cigaban mai haƙan rijiya. Ba duka marubutan zamanin yau mutum zai karanta littattafan su ba ya ga hoton rayuwar Bahaushe sai dai akasin ta. Kai yadda ake rubuta Hausar tasirin baƙin al’adu da maƙota su kan yi naso sosai yadda za ka ji ana Hausa amma ga ta nan dai kamar ana gwaranci. Waɗannan na daga cikin wasu daga dalilan da su ka sanya darajar marubutan zamanin yau faɗuwa a idanuwan jama’a masu ilimi da masu mutunci da masu kishin Bahaushe sosai.

Mene ne burin ka a fagen rubutu?
Buruka na a fagen rubutu su na da yawa kuma mafi yawan su Alhamdulillahi Allah Ya biya mini su tun ina raye. A da can ba ni da burin da ya wuce na ga ana nazarin littattafai na a jami’o’i da kwalejojin ilimi da makarantun sakandare. Allah Ya cika mini wannan buri domin ba ma a nan gida Nijeriya ba har a ƙasashen Turawa irin su Jamus da Poland da Amurika da Indiya da Nepal an yi kuma ana ci gaba da nazarin wasu daga littattafai na. A yanzu dai ba ni da burin da ya wuce na ga rubuce-rubuce na da yanzu haka na fi mayar da hankali a kan su sun zama silar ilmantar da al’umma da kuma bunƙasa musu tattalin arziki. Ina nan ina daf da fitar da wasu littattafai masu ƙoƙarin sauya tunanin al’umma a kan yadda tunani ya ke da tasiri da dangantaka wajen mayar da mutum talaka ko mai arziki. Yadda talauci a yau ya ci lakar al’umma buri na shi ne waɗannan littattafai nawa su farkar da jama’a su kuma nuna wa masu karanta su hanyar zuwa ƙoramar arziki. Littafi na farko a cikin su na kira shi da sunan Zuciyar Mutum Gonarsa, wato irin tunanin da mutun ya ke shukawa a gonar zuciyarsa irin nasara ko arzikin da zai girbe a rayuwar sa.

A matsayin ka na ɗaya daga cikin marubuta da su ka shahara, shin akwai wani shiri da ku ke yi na a gyara ko koyar da marubuta masu tasowa yadda za su inganta rubutun su?
A gaskiya a iya sani na ban san wani ƙoƙari da marubuta a ƙungiyance a yau su ke yi ba don gyara ko koyawa marubuta masu tasowa yadda za su inganta rubutun su. Ni dai a karan kaina na san ina yin ƙoƙarin koyawa matasan marubuta dabarun rubutu a wasu dandali na WhatsApp da na buɗe inda matasan marubuta su ke amfana daga tsofaffin hannu ta hanyar tattaunawa da kuma shirya musu horarwa lokaci zuwa lokaci. A cikin waɗannan dandalai akwai All Poets Network da kuma Muryar Adabi. Masana da marubuta da manazarta sukan haɗu a koyaushe a waɗannan zauruka kuma a gaskiya ana amfanar juna sosai.

Ta ya za a iya dawo da martabar rubutu?
Za a iya dawo da martabar rubutu amma fa tilas ne sai an haɗa kai, an kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe. Hausawa na cewa hannu ɗaya ba shi ɗaukar jinka kuma tsintsiya ɗaya ba ta shara, wato sai masana da manazarta da marubuta sun haɗa kai kowa ya daina yi wa ɗan’uwan sa kallon hadarin kaji.

Daga ƙarshe wace shawara za ka ba wa marubuta ‘yan’uwan ka?
Shawarata ta ɗaya da zan ba wa marubuta ‘yan’uwa na ita ce mu zama ‘yan’uwa masu tuntuvar juna da taimakon juna wajen bai wa junan mu managartan shawarwari. Shawara ta ta biyu kuma ita ce ya kamata mu daina hanzari wajen buga komai mu ka rubuta face mun bayar an tace, an tsefe kuma an gyara sosai kafin mu kai ga bugawa a matsayin littafi. Mu dinga ƙoƙarin halartar taruka na ƙara wa juna ilimi, sannan kuma mu rage haifar wa da kan mu abubuwan da za su bai wa wasu damar ganin wallen mu domin dai masu hikima na cewa sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wajen shiga. In mu ka zama tsintsiya maɗaurin ki guda za mu fi zama kusa da juna da kuma amfanar juna. A ƙarshe shawara ta ga duk marubuta musamman matasa ita ce bincike da yawaita karatu su ne manyan sirrukan da ke sa a rubuta ingantaccen littafi. Wajibi ne mu fahince cewa littafi kamar kan ɗaki ne wanda hannu ɗaya ba ya iya masa.

To madalla. Mun gode
Ni ma na gode