Ƙara wa’adin rijistar zaɓe dama ce ga al’ummar Yobe – Hon. Shariff Abdullahi

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Ɗan takarar kujerar Gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi ya yaba da matakin da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙara wa’adin rijistar katin zaɓe zuwa ƙarshen watan Yuni, 2022. Tare da kira ga ilahirin al’ummar jihar Yobe da qasa baki ɗaya su yi amfani da wannan dama.

Ya sanar da hakan a takardar manema labarai mai ɗauke da sa hannunsa tare da bayyana cewa, “mun yaba wa matakin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙara lokacin rijistar zaɓe zuwa ƙarshen Yunin 2022 babbar dama ce ga al’ummar Jihar Yobe da ƙasa baki ɗaya, kuma nasara ce ga tsarin dimukuraɗiyya.”

Hon. Abdullahi ya ce sanin kowa ne cewa sai ta hanyar katin zaɓe ne al’ummar jihar take da cikakkiyar damar kawo sauyi mai ma’ana a Yobe da Nijeriya, tare da canja gwamnatin da ta kasa inganta rayuwar jama’a zuwa gwamnati mai ƙwazo da kishin al’umma. 

Ya ce, “Saboda haka, wannan dama ce ga al’ummar mu, ƙuri’armu ita ce ‘yancinmu kuma damar da za mu yi amfani da ita wajen kawo shugabanin da za su tausaya mana tare da ciyar da jiharmu gaba, ta bunƙasa.

“Muna kira ga ilahirin al’ummarmu, su fito ƙwansu da ƙwarƙwata, maza da mata waɗanda shekarunsu suka kai, su hanzarta zuwa cibiyoyin sabunta katin zaɓen, domin su karva kuma su zaɓi jam’iyyar PDP domin cigaba da muhimman ayyukan da ta saka a gaba.

“Kar mu manta, zaɓen shugabani nagari wajibi ne ga kowane mutum mai kishin ƙasarsa da al’ummarsa, kuma damar yin hakan ya rataya ne idan kana da katin zaɓe. Al’ummar jihar Yobe dama ce gare mu wadda ya dace mu yi amfani da ita,” ya nanata.