Ƙarancin lantarki: Wasu kamfanoni sun yanke shawarar ficewa daga Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Fiye da makonni uku kenan a ke fama da matsalar ƙarancin wutar lantarki da fetur a Nijeriya, abunda ƙarara ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali. Yanzu haka dai kamfanoni da dama sun dakatar da ayyukansu, yayin da wasu kuma ke shirin ƙaura zuwa maƙwabtan ƙasashe.To ko yaya girman matsalar take a masana’antun jihar Kano? 

Gidan Rediyon rfi ya rawaito a shafinsa na yanar gizo cewa, wani Kamfanin sarrafa auduga a jihar Kano mai suna Amarya Cotton sun yanke shawarar za su tattara komatsensu su koma ƙasar Chadi domin cigaba da harkar kasuwancinsu. 

Shugaban Kamfanin Amarya Cotton mai suna, Rabi’u Ibrahim ya bayyana wa majiyarmu cewa, ƙarancin wutar lantarki da ƙarancin man fetur ya sanya kamfaninsu ya rage awanin da yake aiki a kullum sannan sun dakatar da wasu daga cikin ma’aikatansu haka kuma a yanzu suna shawara komawa ƙasar Chadi domin cigaba da aikinsu. 

Alhaji Rabi’u Mamallakin Amarya cotton ya ƙara da cewa, a yanzu haka akwai ma’aikata 200 a ƙarƙashin kamfaninsa. Kuma ya nuna fargabarsa ta yadda waɗancan ma’aikatan nasa za su rasa ayyukansu idan hakan ta faru. 

Hakazalika, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta gyara matsalar saboda cigaban ƙasar. Inda ya bayyana cewa: “Shi ya sa kullum muke kira ga gwamnati da ta yi wani abu a kai. Domin idan muka rufe kamfaninmu ya za ta yi da waɗannan mutane 200?”

Wannan matsala dai ta mamaye dukkan masana’antu a ƙasar nan. Wato dai abinda yake a gidan ƙaura, shi ne dai a gidan Goje. 

Haka, majiyarmu ta zanta da Alhaji Aminu Ɗan Rahmatu mamallakin kamfanin shinkafa na ABD Rice wanda ya bayyana cewa, a ‘yan kwanakin nan ba sa samun yin ayyuka da dama saboda matsalar wutar lantarki. A cewar sa sun shiga damuwa sosai saboda wutar ba a samun ko ta awa biyar a rana. Wannan shi ya sa mutane da dama ba za su iya ba. Don haka, masana’antu da dama za su iya durƙushewa. 

Miliyoyin iyalai ne dai suka dogara da aikin masana’antu a matsayin sana’ar dogaro da kai a Nijeriya. Kuma suna fuskantar barazanar asarar aiki matuƙar mahukuntan Nijeriya ba su taka wa matsalar wutar lantarkin birki ba. Kuma ko ba a faɗa ba, mun san matsalar rashin aikin yi ta na daga manyan musabbaban kawo matsalar rashin tsaro a Nijeriya.