Ƙarancin mai na cigaba da ta’azzara duk da alƙawarin NNPC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Duk da tabbacin da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayar na cewa za a kawo ƙarshen ƙarancin man fetur a ƙarshen watan Fabrairu, amma har yanzu ’yan Nijeriya na fuskantar wahalar samun man. Shugaban kamfanin mai na NNPC Mele Kyari, ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin man fetur a ranar 16 ga watan Fabrairu, inda ya bada tabbacin kawo ƙarshen ƙarancin man nan da mako guda. Ya shaida wa kwamitin cewa tuni kamfanin ya karɓi lita biliyan 2.1 da za a raba domin daidaita al’amura.

Ƙaranci yana ƙara muni:
Duk da tabbacin, ƙarancin ya yi nisa daga kusan makonni uku bayan haka. Ziyarar da Blueprint ya kai wasu gidajen mai da ke kewayen Abuja, babban birnin ƙasar, Jihar Kaduna da sauransu, a ranar Laraba, ya nuna cewa, al’amura na ƙara ta’azzara yayin da masu ababen hawa ke shafe sa’o’i da dama suna jiran shan mai. Lamarin dai ya yi muni matuƙa, ta yadda masu ababen hawa da kuma dillalan kasuwar bayan fage a wasu lokutan suke kwana a gidajen mai a wasu sassan babban birnin tarayya Abuja da zummar samun mai.

Haka nan abin da ya fi muni shi ne masu ababen hawa, waɗanda ba wai kawai sun ninka kuɗin da suka saba sayan feyur ɗin ba ne kawai, amma kuma sukan jira sa’o’i a gidajen mai don saya. Abin da ya fara a matsayin samar da man fetur mara kyau shi ne daga baya ya koma ƙarancinsa.

Lokacin da Blueprint Manhaja ta isa gidan man A.A Rano da ke kan hanyar Nyanya-Karshi da misalin ƙarfe 12:24 na yammacin Laraba, gidan man yana rarraba mai ga masu ababen hawa a cikin ruɗani saboda wasu daga cikin masu ababen hawa sun yi layi tun ƙarfe 5:30 na safe. Wani direban babur mai uku (wanda aka fi sani da Keke NAPEP), wanda ya bayyana sunansa da Sule, ya ce, tun safe bai yi aiki ba saboda yana buƙatar ya cika tankinsa domin sayen fetur a wurin ’yan kasuwar bayan fage ba riba.

Mutane sun koka:
Halin da ake ciki na man fetur ya sanya miliyoyin matafiya cikin mawuyacin hali, inda da yawa ke zargin gwamnati da rashin kula da halin da suke ciki. Wani matafiye mai suna Ahmad ya bayyana cewa, lamarin ba ma sauƙi domin yana ta munana ne duba ga yadda layuka ke da ƙaruwa a gidajen mai. Da ya ke ba da labarin abin da ya faru, Ahmad ya ce, ya kusa yin faɗa da wani direban tasi da ya ɗaura ɗamarar karɓar Naira 500 daga gare shi maimakon N250 da ake karɓa.

Binciken da muka gudanar ya nuna cewa, a ranar Talata masu ababen hawa da sauran masu amfani da man fetur a unguwar Rigasa da ke Jihar Kaduna sun sayi litar man fetur a kan Naira 500 a kasuwar bayan fage, saboda qarancin man fetur ɗin ya ci tura. An tattaro cewa, a wasu gidajen mai da ake sayar da mai, ya kasance tsakanin Naira 250 zuwa N300 kan kowace lita a kasuwar bayan fage kamar yadda ya zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto.

A Jihar Kaduna kuwa, lamarin ya munanan mutuƙa, domin a wasu gidajen mai ma fetur ya kai naira 270 a kowanne lita. Wakilin Blueprint Manhaja ya zagaya cikin garin Kaduna inda ya tabbatar da cewa a wasu gidajen man fetur abin sai dai addu’a, kamar a gidan mai a A.A Rano da ke Kawo, wasu kan kwana a kan layi kuma da safiyar ma sai hantsi ya fito za su sha man.

Farashin litar man fetur a hukumance a Nijeriya N165 ne:
Mummunan halin da ake ciki ya tilastawa masu motoci masu zaman kansu da yawa yin fakin motocinsu suna hawan na haya don zirga-zirgar kasuwancinsu, lamarin da ya yi tashin gwauron zabin shiga ciki da na tsaka-tsaki da kusan kashi 100 cikin 100. Har ila yau, lamarin ya yi tasiri mai yawa akan kayan abinci, kayayyaki da ayyuka tare da haɓakar farashi na komai a Nijeriya. Wasu daga cikin jama’a da suka zanta da Blueprint Manhaja, sun buƙaci gwamnati da ta gaggauta samar wa al’ummar ƙasar man fetur a ishassashe, domin sauƙaƙa munanan illolin da ya ke haifarwa a zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.

Sai dai Kamfanin na NNPC ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa za a kawo ƙarshen ƙarancin man a cikin wannan mako, inda ya ƙara da cewa, ana ƙoƙarin fitar da isasshiyar man da zai cika ishe ko ina don magance ƙarancin man fetur ɗin da wasu ƙungiyoyi ke shigo da su ƙasar nan, ƙoƙarin da ta ke yi don tsaftace halin da ake ciki. A halin da ake ciki kuma, ƙungiyar tsoffin ’yan jarida ta ƙasa (NALVEJ) reshen jihar Kwara ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta nemo bakin zaren warware matsalar man fetur da ta addabi ƙasar nan. Ƙungiyar ta yi nuni da cewa, ’yan Nijeriya musamman al’ummar jihar Kwara na cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin man fetur. Hakan ya kasance wani ɓangare na ƙudurorin da aka cimma a ƙarshen taron wata-wata na ƙungiyar da aka gudanar a ranar Laraba a Ilorin, jihar Kwara.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ƙarshen taron kuma mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Alhaji Tunde Akanbi da sakataren yaɗa labarai, Alhaji Abdullahi Olesin, ƙungiyar ta koka da cewa tsananin zafi da ake fama da shi a Ilorin ya ƙara dagula al’amuran mazauna garin. An yi nuni da cewa, wani hatsarin mota da ya afku a unguwar filin tashi da saukar jiragen sama na garin Ilorin a baya-bayan nan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara, sakamakon ƙarancin man fetur da ya tilastawa ɗaya daga cikin direbobin motocin da abin ya shafa ya ajiye jarkar mai a cikin motarsa.

Har ila yau, ta ɗora alhakin ƙarancin man fetur da mutuwar wani mutum, wanda ya faɗo daga wani bene mai hawa biyu bayan ya kwanta a titin gidansa da ke Ilorin saboda zafi.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati a dukkan matakai da ta sanya ido kan harkokin dillalan mai tare da tabbatar da cewa sun ba da man a cikin tankunansu da kuma farashin man fetur a hukumance. Haka zalika, akwai fargabar cewa ƙarancin kayayyaki na iya ƙara dagula halin da Nijeriya ke ciki a halin yanzu.

Rahotanni sun ce faɗan da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine zai shafi masu samar da kayayyaki saboda tace kayayyakin da ke fitowa daga ƙasashen da ke gaba da juna da makwabtanta na iya fuskantar wasu tsaiko. Har ila yau, akwai fargabar cewa rashin isassun ɗanyen mai daga NNPC ba zai taimaki lamarin ba. A ƙarƙashin shirinta na kai tsaye (DSDP), rahotannin sun nuna cewa, kamfanin na NNPC na da giɓi na kaya kusan 17 a cikin aikin da DSDP ɗin ta ke yi saboda ƙarancin man da ake haƙowa.

Ƙungiyar ta OPEC ta yanke yarjejeniyar haƙo mai tare da lalata bututun mai, da kuma gyaran bututun mai akai-akai ya yi matuƙar tasiri ga haƙo mai a Nijeriya, wanda ya faɗi zuwa kusan ganga miliyan 1.5 a kullum.

Kamfanin NNPC ya ba da haƙuri:
Ko da yake kiran da aka yi wa mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Garba Deen Mohammed ya ci tura, amma kamfanin ya nemi a yi haƙuri da fahimta. Har ila yau, ya ce, cikakken daidaita sassan da ke ƙarƙashin ƙasa zai bunƙasa ƙarfin tacewa a cikin gida na ƙasar.

Babban Daraktan Rukunin NNPC Mustapha Yakubu ne ya bayyana haka a wannan Laraba yayin wani taron tattaunawa da ake yi a Babban Taron na Ƙasa (NIES) a Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai na NIjeriya (NAN) ya ruwaito cewa, taken taron shi ne, ‘Revitalising the Industry: Future Fuels and Energy Transition.’

Yakubu ya yi nuni da cewa, yadda za a kawar da tsaftar muhallin da ke ƙarƙashin ƙasa zai ƙarfafa gwiwar kafa matatun mai na zamani da na taki a ƙasar nan. Ya ce, NNPC na da hurumin kare tsaron lantarkin Nijeriya kuma za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga ƙoƙarin da ake yi na ƙara darajar ɗanyen man da ƙasar ke haƙowa.

A wani labarin kuma, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya buƙaci gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ta miƙa wa majalisar dokokin ƙasar wani ƙudiri na yin kwaskwarima ga dokar masana’antar man fetur (PIA). Lawan ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa na ɗan lokaci kafin ya miƙa buƙatar shugaban ƙasa na gyara dokar kasafi ta 2022 ga kwamitin kasafin kuɗi bayan da ƙudirin ya tashi a karatu na biyu.

Ya ce, buƙatar neman gyara ga PIA, za ta bai wa majalisar dokokin ƙasar damar tsawaita tsarin bayar da tallafin a cikin dokar yadda ya dace da buƙatar shugaban ƙasa na ƙarin Naira tiriliyan 2.557 domin cike tallafin mai a kasafin kuɗin 2022 daga watan Yulin wannan shekara. Ana sa ran tsarin tallafin na yanzu zai wuce a watan Yuni, 2022, daidai da tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur.

A wata wasiƙa da shugaba Buhari ya aikewa majalisar dokokin ƙasar mai ɗauke da kwanan watan 10 ga watan Fabrairu, 2022, ya buƙace ta da ta ƙara tanadin naira tiriliyan 2.557 domin samar da tallafin man fetur a tsarin kasafin kuɗin shekarar 2022 daga watan Yuli na wannan shekara. Lawan ya umarci kwamitocin mai da iskar gas na Majalisar Dokoki ta ƙasa da su shigar da ɓangaren zartarwa kan ƙudirin yi wa hukumar PIA kwaskwarima domin yin daidai da buƙatar Shugaban Ƙasaasa.