Ƙasar Amurka ce mai kisan ƙare-dangi

Daga CRI HAUSA

A ranar 2 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fidda dogon bayani mai taken “Shaidu game da yadda ƙasar Amurka ta yi wa mazaunan India kisan ƙare-dangi”, inda ta fidda cikakkun bayanai da shaidu kan yadda ƙasar ta yi musu kisan ƙare-dangi da goge al’adunsu.

Bisa ƙididdigar da aka yi, daga shekarar 1492 zuwa farkon ƙarni na 20, yawan al’ummomin Indian ya ragu matuka daga miliyan 5 zuwa dubu 250, sabo da raguwar yawan al’umma, Amurka ta tilastawa al’ummomin Indian daidaitawa da goge al’adunsu, lamarin da ya sa, ta kawar musu ’yancin kai baki ɗaya, har ya kai su ga rasa iko wajen raya tattalin arziki. Kuma, gwamnatin Amurka ta hana yaran Indian amfani da harshensu.

Ko da yake, a halin yanzu, ƙasar Amurka tana ci gaba da nuna fuska biyu kan batun haƙƙin bil Adama, batutuwan da suka faru cikin tarihinta sun nuna mana cewa, ita ce ta yi wa mazaunan Indian kisan ƙare-dangi, kuma, bai dace ta kira kanta da “Mai kare haƙƙin dan Adam” ba.

Fassarawa: Maryam Yang