Ƙasar Sin na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya tsaro a duniya

Daga CRI HAUSA

Wani rahoton aiki da kotun kolin jama’a ta ƙasar Sin (SPC) ta fitar Talatar nan, na nuna cewa, ƙasar Sin na daya daga cikin ƙasashen da suka fi zaman lafiya a duniya.

Rahoton wanda aka miƙa wa majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin domin tattaunwa, ya bayyana cewa, adadin manyan laifuffuka iri-iri guda takwas, kamar kisan kai, da fyaɗe da kuma satar mutane, ya ragu matuka, yayin yawan irin waɗannan laifuffuka da ke cikin laifuffuka duka shi ma ya ragu sosai

A cewar rahoton kotun kolin, ƙasar Sin ta sanya hukunci mai tsauri kan laifuffukan da suka shafi cin hanci da rashawa kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada, A hannun guda kuma a shekarar 2021, kotunan ƙasar Sin, sun kammala yanke hukunci kan ƙararraki 23,000 da suka shafi cin hanci da rashawa, waɗanda suka shafi mutane 27,000.

Fassarawa: Ibrahim