Ƙasar Sin na ba da taimako ga jama’ar ƙasar a fannin samun guraben aikin yi

Daga BELLO WANG

A ganin Sinawa, shan aiki ya fi zaman kashe wando. A titunan biranen ƙasar, ana iya ganin yadda motoci da mutane ke wucewa cikin sauri. Kuma da wuya ne a ga wani matashi yana zama a gefen hanya ba tare da gudanar da wani aiki ba. Wannan ya nuna wani yanayin da ƙasar ke ciki: mutanen ƙasar na son aiki, kana hukumar ƙasar ta samar musu da isassun damammaki.

Cikin rahoton ayyukan gwamnati da ƙasar Sin ta gabatar a kwanan baya, ta sanya burin samar da ƙarin guraben aiki fiye da miliyan 11, da kare jimillar yawan rashin aikin yi a ƙasa da kashi 5.5% a bana. To ko ta yaya ƙasar za ta cimma wannan buri?

Da farko dai, za ta ba da taimako ga kamfanoni masu zaman kansu don su bunƙasa yadda ya kamata, ta yadda za su iya samar da guraben aikin yi. A nan ƙasar Sin, akwai matsakaita da kananan kamfanoni miliyan 140, waɗanda ke samar da guraben aikin yi da yawansu ya kai kashi 85% a ƙasar. Sai dai waɗannan kamfanoni sun fi jin raɗaɗin mummunan tasirin da annobar COVID-19 da lalacewar tattalin arzikin duniya ke haifarwa. Saboda haka gwamnatin ƙasar Sin ta ɗauki niyyar rage musu haraji da kuɗin da za su biya, waɗanda yawan su zai kai kimanin dala biliyan 393.5, da samar wa kamfanonin ƙarin bashi, don taimaka musu wajen jure wahalar da suke fuskantar.

Ban da haka, don samar da ƙarin guraben ayyukan yi, ya kamata a haɗa ƙarfin ɓangarori daban daban na al’umma. Misali, a birnin Tianjin na ƙasar Sin, ana samun cibiyoyin taimakawa ɗalibai samun aikin yi a cikin jami’o’i daban daban, wadanda su kan gayyaci kamfanoni zuwa ɗaukar sabbin ma’aikata a cikin jami’o’in. Kana idan wani ɗalibi bai samu gurbin aikin yi ba a lokacin da ya kammala karatunsa, to, gwamnati za ta ba shi taimako, inda za ta ba shi damar halartar kwas na koyon sanin makamar aiki a wasu kamfanoni.

Cikin wa’adin kwas din, ɗalibin na samun tallafin kuɗi daga gwamnati a kai a kai. Sa’an nan bayan da aka kammala kwas, kamfanin da ya ɗauki ɗalibin a matsayin sabon ma’aikacinsa shi ma zai samu lada.

Ban da haka kuma, su hukumomi na matakin ungwanni suna ba da taimako ga nakasassu, da magidantan da babu mutane masu aiki, don su samu aikin yi, da damar fid da kansu daga ƙangin talauci.

Sa’an nan don raya ɓangaren samar da guraben aikin yi, dole ne a gudanar da aikin horaswa da kyau. Domin a wasu wuraren dake fama da koma bayan tattalin arziki, mutane su kan gamu da matsala yayin da suke neman ayyukan yi ne sakamakon rashin sanin fasahohi na wasu ayyuka. Don daidaita wannan matsala, ƙasar Sin za ta ware kuɗin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 15.7 a bana, don bai wa mutanen ƙasar damar shiga kwas, inda za su koyi wata fasahar aiki ta musamman, ko kuma inganta fasahohinsu.

Ci gaban ɓangare mai alaƙa da yanar gizo ta Internet, shi ma ya samar wa Sinawa da wasu sabbin guraben aikin yi, irinsu masu gabatar da shirye-shiryen bidiyo da masu sayar da kayayyaki a shafukan yanar gizo, da dai sauransu. Don tabbatar da haƙƙi da moriyar waɗannan mutane, ƙasar Sin ta ɗauki niyyar daidaita manufofi, don samar musu da hidimomin inshora, ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu hankali a kwance.

A cewar firaministan Kasar Sin Li Keqiang, “samar da guraben aikin yi ba kawai yake shafar zaman rayuwar jama’a, har ma da aikin raya ƙasa”. Bayan da wani mutum ya samu aikin yi, to, zai samu kuɗin shiga, gami da damar samar da kayayyaki da hidimomi ga al’umma. Kana yadda ake samun kuɗin shiga, zai taimakawa tabbatar da kwanciyar hankali, da raya ɓangaren sayayya, da janyo jari, waɗanda za su tabbatar da ci gaban tattalin arzikin wata ƙasa.

Za mu iya takaita maganar zuwa: Daidaita batun samun kuɗin cin abinci na jama’a, tamkar daidaita maganar samun ci gaban ƙasa ne. Wannan shi ne dalilin da ya sa ƙasar Sin ke matuƙar ƙoƙarin samar da guraben aikin yi ga al’ummarta.