Ƙasar Sin na tallafa wa gina “ganuwar bishiyoyi a Afirka”

Daga CMG HAUSA

Yanzu haka, taron UNCCD COP15, wato taron masu ruwa da tsaki na yarjejeniyar hana kwararowar hamada ta MƊƊ karo na 15, na gudana a birnin Abidjan, hedkwatar tattalin arziki ta ƙasar Cote d’Ivoire, taron da ke mai da hankali a kan samar da wani dauwamammen shiri na daidaita matsalar farfaɗo da filayen ƙasa da ma yaƙi da fari.

Tun bayan da ƙasar Sin ta daddale yarjejeniyar hana kwararowar hamada ta MDD, har kullum tana ƙoƙarin sa kaimin aiwatar da yarjejeniyar, a yayin da kuma take haɗa kan ƙasashen Afirka wajen aiwatar da shirin gina “ganuwar bishiyoyi” a Afirka, don kare kwararowar hamada, shirin da ake kira “Great Green Wall” a Turance.

A ranar 13 ga watan Afrilun wannan shekara, an shirya kwas na tallafawa shirin a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, kuma jami’ai sama da 20 da suka zo daga ƙasashen Burkina Faso, da Chadi, da Mali, da Nijer, da Mauritania, da Senegal sun halarci kwas ɗin ta yanar gizo.

A gun taron da ke gudana a wannan karo, ƙasar Sin ta gabatar da wasu shawarwari uku, ciki har da inganta haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, da sa ƙaimi ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, sai kuma a inganta dokokin ƙasa da ƙasa, shawarwarin da suka ƙara samar da kuzari ga ƙoƙarin da ake yi na kiyaye muhallin nahiyar Afirka.

An dai ƙaddamar da taron a ranar 9 ga wata, kuma za a kammala shi a ranar 20 ga wata.

Mai Fassara: Lubabatu