Ƙasar Sin ta cimma manufar shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin ƙanƙara

Daga CRI HAUSA

Yayin da ƙasar Sin ke neman baƙuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022, ta yi wa ƙasashen duniya alƙawarin shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin ƙanƙara. Bayan da ta samu nasarar karɓar baƙuncin shirya gasar a shekarar 2015 har zuwa yanzu, wasannin ƙanƙara sun zama wata hanyar jin daɗin zama a tsakanin al’ummar ƙasar Sin.

Adadin ƙididdiga ya nuna cewa, tun bayan da ƙasar Sin ta samu damar karɓar baƙuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 ya zuwa watan Oktoban shekarar 2021, yawan mutanen da suka shiga wasannin ƙanƙara ya kai miliyan 346 a duk ƙasar baki ɗaya. Sin ta cika alƙawarinta na shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin ƙanƙara, wanda shi ne sakamako mafi girma da aka samu sakamakon shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing.

Aikin yawon shakatawa a wurare masu ƙanƙara ya samu saurin bunƙasuwa a ƙasar Sin. Alƙaluma sun nuna cewa, yawan zirga-zirgar mutanen da suka shaƙata a wurare masu ƙanƙara ya kai miliyan 230 a kasar Sin, kana yawan kuɗin shigar da aka samu a fannin ya wuce kuɗin Sin RMB yuan biliyan 390. An ƙiyasta cewa, yawan zirga-zirgar mutanen da za su shakata a wurare masu ƙanƙara zai iya kaiwa miliyan 305 daga shekarar 2021 zuwa 2022 a ƙasar Sin.

Wasannin ƙanƙara na kara taka muhimmiyar rawa wajen farfado da yankunan karkara, sauya salon raya wurare da tabbatar da samun bunƙasuwar tattalin arziki mai ɗorewa da ci gaban ƙasa mai inganci.

Fassarawa: Tasallah Yuan