Ƙasar Sin ta kammala aikin bada taimakon abinci a Kenya

Daga CRI HAUSA

Gwamnatin ƙasar Kenya da ofishin jakadancin ƙasar Sin a ƙasar, sun sa hannu kan takardar shaidar miƙa abincin da yawansa ya kai ton 11835, wanda darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 12 jiya Litinin a birnin Nairobi. Wannan ya shaida cewa, an cimma nasarar kammala aikin ba Kenya taimakon abinci cikin gaggawa.

A shekarar 2018 ne gwamnatin Sin ta sa hannu kan takardar aikin, inda ta bai wa Kenya abinci a rukunoni 8.

An ɗauki shekaru da dama ana fama da fari a ƙasar ta Kenya. A watan Satumban shekarar 2021 ne shugaban Kenya ya sanar da ayyana fari a matsayin bala’in da ya shafi ƙasar baki ɗaya. A ranar 8 ga wata kuma, hukumar tsara shiri kan abinci ta duniya ƙarƙashin inuwar MDD ta bayyana cewa, wasu ƙasashe da ke yankin ƙahon Afirka suna fama da tsananin fari, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, inda mutane miliyan 13 suke fama da mummunar matsalar ƙarancin abinci a ƙasashen Habasha, Kenya, da Somaliya.