Ƙasashen tsibiran Tekun Pasifik sun fi buƙatar Sahihiyar gudummawa daga ƙasar Amurka

Daga CMG HAUSA

Daga ranar 28 zuwa 29 ga watan Satumba, an gudanar da taron ƙoli na ƙasar Amurka da ƙasashen tsibiran tekun Pasifik karo na farko a birnin Washington, inda shugaban ƙasar Amurka Joseph Biden ya bayyana cewa, makasudin gudanar da taron ƙolin shi ne, zurfafa dangantakar dake tsakanin Amurka da ƙasashen tsibiran tekun Pasifik.

Kana ya sanar da samar da gudummawar da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 810 ga ƙasashen tsibiran tekun Pasifik don inganta haɗin gwiwarsu a fannonin tinkarar sauyin yanayi, da tattalin arzikin teku da sauransu.

Kafofin watsa labaru na ƙasar Jamus sun ruwaito cewa, gwamnatin ƙasar Amurka ta samarwa shugabannin ƙasashen tsibiran tekun Pasifik damar halartar taron da kuma gudummawar kuɗin dala, don hana Sin yin babban tasiri a yankin tekun Pasifik.

Abu ne mai kyau Amurka ta samar da gudummawa ga ƙasashen tsibiran tekun Pasifik, amma ƙasashen tsibiran tekun Pasifik ba sa buƙatar alƙawarin fatar baki, kuma ba sa son zama wani ɓangaren da ake amfani da shi don hana ci gaban ƙasar Sin, kuma sun fi bukatar sahihiyar gudummawa bisa yanayinsu na samun ci gaba.

Idan ƙasar Amurka tana son taimakawa ƙasashen tsibiran tekun Pasifik, ya kamata ta yi ayyuka huɗu, wato samar da haƙiƙanin gudummawa bisa alƙawarin da ta yi, da ɗaukar alhakin dake wuyanta game da tinkarar sauyin yanayi, da ɗaukar matakai wajen kare yanayin hallitun teku, da kuma girmama ƙasashen na tsibiran tekun Pasifik, a maimakon maida su matsayin wani ɓangaren da ake amfani da shi a harkokin siyasa.

Mai fassara: Zainab