Ƙasungumin mai safarar hodar Ibilis na duniya ya shiga hannu a Colombia

Jami’an tsaron Colombia sun samu nasarar cafke ƙasungumin mai fataucin muggan wayoyi mafi shahara da aka fi sani da Otoneil, wanda suka daɗe suna farautarsa, la’akari da cewar a halin yanzu shi ke kan gaba wajen safarar hodar iblis a duniya.

Hukumomin tsaro sun ce an kama Otoniel da asalin sunansa shi ne Dairo Antonio Usuga, a kusa da ɗaya daga cikin manyan ofisoshinsa a yankin Necocli, dake kusa da kan iyaka da Panama.

Sojoji aƙalla 500 tare da jirage masu saukar ungulu 22 gami da taimakon hukumomin tsaron Ingila da Amurka ne suka kai samamen da ya basu nasarar cafke Otoniel a yankin Necocli, inda a ƙoƙarin hakan ɗan sanda ɗaya ya rasa ransa.

Hotunan da gwamnati ta fitar sun nuna Otoniel mai shekaru 50 cikin ankwa yayin da kuma sojoji ke kewaye shi.