Ƙoƙarin Sin na neman samun jituwa tsakanin ɗan Adam da muhallin duniya

Daga BELLO WANG

Kogin Yangtse, wani kogi ne na ƙasar Sin, wanda tsawonsa ya kai fiye da kilomita 6300, ko kuma mu ce kogi ne mafi tsawo na 3 a duniya.

An taba samun mutane fiye da dubu 200, da suke gudanar da aikin kamun kifi a kogin Yangtse.

Amma sannu a hankali, kifayen da ke cikin kogin ya ragu, sakamakon yawan sun kifi fiye da kima, da shigar da gurbataccen ruwa cikin kogin, lamarin da ya sanya masunta cikin wani yanayi na kunci.

Sai dai daga bisani, an fara aiwatar da wata doka ta tsawon shekaru 10, ta hana kamun kifi a kogin Yangtse, tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021, a matsayin ɗaya daga cikin matakan da ƙasar ke ɗauka, da zummar kare muhallin yankin kogin Yangtse, da kyautata zaman rayuwar mutane masu ruwa da tsaki.

Gwamnatin ƙasar Sin ta taimaki masunta fiye da dubu 200, wajen samun sabbin guraben aikin yi a sauran sana’o’i daban-daban.

Kana daga cikinsu, mutanen da suka tsufa, an ba su damar yin ritaya, inda ake samar musu da kuɗin fensho na tsofaffi a duk wata, don tabbatar da ingancin rayuwarsu.

A sa’i ɗaya kuma, ana ta samun ci gaba a ƙoƙarin kare muhallin yankin kogin Yangtse, inda ake samun ruwa mai tsabta, da ƙarin kifaye.

Yadda aka kyautata muhallin yankin kogin Yangtse, ya nuna wani abun da Sinawa suka ɗora muhimmanci a kai, yayin da suke neman zamanintar da ƙasarsu, wato ƙoƙarin neman samun jituwa tsakain ɗan Adam da muhalli.

Ana ƙoƙarin raya tattalin arzikin ƙasa ne don kyautata zaman rayuwar jama’arta, kana ba a taba raba zaman rayuwa mai inganci da muhalli mai kyau ba.

Sai dai ta yaya ake iya raya tattalin arziki, gami da kare muhallin halittu, a lokaci guda?

Tabbas, Sinawa suna ƙoƙarin gudanar da bincike da gwaje-gwaje a wannan fanni.

Akwai wani babban tabki mai suna Qiandao a gundumar Chun’an ta lardin Zhejiang dake gabashin ƙasar Sin.

Wani wuri ne mai ni’imtaccen muhalli, da duwatsu da tabkuna masu kyan gani.

Sai dai manufar kare muhalli ta takaita damammakin da mutanen wurin suke da shi na raya masana’antu.

Wannan yanayi ya sa mutanen wurin karkarta ga sauran dabaru don raya tattalin arziki.

Idan mun ɗauki wani ƙauye mai suna Xiajiang dake gundumar Chun’an a matsayin misali, muka tantance sana’ar da mazauna ƙauyen suka ɗauka wajen raya ƙauyen, za mu ga babbar sana’ar da suka ɗauka ita ce yawon shakatawa.

A cikin ƙauyen, kusan kowane magidanci na kula da wani ƙaramin otel, a karkashin jagorancin hukumar ƙauyen.

Ko da a shekarar 2020, wani lokaci da aka fi fama da mummunar illar da annobar COVID-19 ta haifar, ƙauyen ya janyo mutane kimanin dubu 770, wadanda suka ziyarci ƙauyen, tare da sayen kayayyaki, da cin abinci, da jin dadin hutunsu.

Sa’an nan, a garin Linqi dake dab da ƙauyen Xiajiang, mutane sun fi dora muhimmanci kan aikin dasa wasu bishiyoyi, da sarrafa su zuwa magungunan gargajiya.

Yanzu wasu magungunan gargajiya guda 6 da ake samarwa a garin, suna samun karbuwa sosai a kasuwannin ƙasar Sin.

Ta sana’ar yawon shakatawa, da sarrafa magungunan gargajiya, ana samar da guraben aikin yi ga jama’a, da hanyoyin da ake bi wajen raya tattalin arziki, ba tare da gurɓata muhalli ba.

Sa’an nan a wajen tabkin Qiandao, yadda ake ƙoƙarin kare tsabtar ruwan tabkin, ba ya nufin hana mutum cin gajiyar albarkatun da ke akwai.

Wani abun da ake fitarwa daga cikin ruwan tabkin Qiandao, wanda ya fi shahara a kasuwannin ƙasar Sin, shi ne wani nau’in kifin da ake kira Bighead Carp.

Sinawa suna son cin naman wannan nau’in kifi sosai.

Ban da haka kuma, ta hanyar kiwon kifin Bighead Carp da ake yi a tabkin, ana iya samar da gudunmowa ga ƙoƙarin tabbatar da tsabtar ruwan tabkin.

Saboda ƙananan kifayen Bighead Carp kilo ɗaya, su kan iya cinye kimanin kilo 40 na ciyayin ruwa na Algae mai gurbata muhalli, yayin da suke girma.

Ban da wannan kuma, yunƙuri na kiyaye tsabtar ruwa bai hana su gudanar da aikin gona ba.

A ƙauye Anyang, duk a ƙarƙashin gundumar Chun’an, ana ƙoƙarin yayata wata fasahar aikin gona ta zamani ta kare tsabtar ruwan kogi.

Ta wannan fasaha, ana daidaita nau’ikan ganyayen da ake shukawa, ta yadda ake samun damar rage yin amfani da maganin kashe ƙwari mai guba, da takin zamani.

Ban da wannan kuma, an dasa wasu bishiyoyi na musamman a gefen gonaki, waɗanda suke taimakawa wajen tace sinadarai masu guba daga cikin ruwan da ya fito daga cikin gonaki.

Ta waɗannan hanyoyi, an rage tasirin da aikin gona yake wa muhallin halittu ƙwarai da gaske.

Yayin da ƙasar Sin ke neman ganin samun ci gaban masana’antu, da wadatar da jama’arta, da kare muhallin halittu a lokaci guda, tana kuma son raba fasahohi masu kyau da ta samu ga sauran ƙasashe masu tasowa, ta yadda za a cimma burin samun ci gaba mai ɗorewa a ƙasashe daban daban.

Idan mun ɗauki nahiyar Afirka a matsayin wani misali.

Cikin shekarun da suka gabata, ƙasar Sin ta dukufa wajen taimakawa ƙasashen Afirka wajen raya makamashi mai tsabta.

A Bangui, fadar mulkin ƙasar Afirka ta tsakiya, an daɗe ana fama da matsalar ƙarancin wutar lantarki. A baya, magidantan birnin kimanin kashi 35% kacal ne ke samun hidimar wutar lantarki.

Sai dai a ranar 15 ga watan Yunin bana, tashar samar da wutar lantarki mai amfani da zafin rana ta Sakai, da ƙasar Sin ta ba da ita a matsayin tallafi ga ƙasar Afirka ta Tsakiya ta fara aiki.

Daga bisani, kimanin kashi 2 cikin kashi 3 na ɗaukacin magidantan birnin Bangui, sun samu damar yin amfani da wutar lantarki, lamarin da ya sauƙaƙa zaman rayuwarsu matuƙa.

Ban da wannan kuma, a ƙasar Uganda, wani kamfanin ƙasar Sin na ci gaba da ƙoƙarin gina tashar samar da wutar lantarki mai amfani da ƙarfin ruwa ta Karuma.

Ana shirin ƙaddamar da wannan tasha a watan Oktoba da muke ciki, inda za ta zama tashar samar da wutar lantarki mafi girma a ƙasar Uganda.

Yadda ake yin amfani da ƙarfin ruwa maimakon makamashi na kwal wajen samar da wutar lantarki, yana taimakawa wajen kare muhalli sosai.

Ban da wannan kuma, yayin da ake gina tashar, an keɓe hanyoyin da dabbobi za su bi, don magance matsalar tare musu hanyar ƙaura.

Haka zalika, an sanya wasu manyan injuna a wani wurin dake da nisan mita 80 a ƙarƙashin ƙasa, don kare dazuzzuka da halittun dake doron ƙasa.

A ganin Sinawa, duniyarmu tamkar ƙauye ɗaya ne ga ɗaukacin bil Adama.

Dalilin raya tattalin arziki, gami da kare muhallin halittu a lokaci guda, shi ne neman tabbatar da makoma mai haske ta dan Adam.

Ya kamata mu haɗa kai, don tabbatar da samun jituwa tsakanin ɗan Adam da muhallin halittu, da kiyaye hakan har abada.

Mai fassara: Bello Wang