Ƙungiyar Fulani ta yaba wa Gwamna Buni bisa kafa ginshiƙin fahimtar juna

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta ‘Kulen Allah Cattle Rearers Association Of Nigeria’ (KACRAN) yaba wa Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Riƙo na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Hon. Mai Mala Buni bisa kafa ginshikin samar da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma a jihar Yobe.

Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Hon. Khalil Mohammed Bello ne ya bayyana haka ga manema labarai a Damaturu ranar Talatar da ta gabata, inda ya buƙaci sauran gwamnatocin ƙasar nan su yi koyi da irin manufofin Gwamnatin Jihar Yobe a ƙarƙashin Gwamna Buni.

Hon. Khalil, ya fara da yaba wa Gwamnan na Yobe tare da yin kira ga sauran gwamnonin Arewa da ma gwamnatin tarayya da su yi koyi da shi wajen ɗaukar matakan daƙile rikicin manoma da makiyaya a faɗin jihar Yobe tare da ƙoƙarin inganta harkokin kiwo da rayuwar makiyaya don kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da ke gudana a faɗin ƙasar nan.

Ya ce, “Jihar Yobe ta na daga cikin jihohin da ke sahun gaba a ƙasar nan wajen kiwon dabbobi wadda wasu jihohi da dama suka dogara da ita ta fuskar samar da nama ga al’umma. Wanda bisa ga haka, a kasafin kuxin 2021 Gwamna Buni ya ware kaso na musamman domin bunqasa harkokin kiwon dabbobi da noma a jihar.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Kaɗan daga cikin tanadin da kasafin ya ƙunsa shi ne samar da wadataccen ruwa mai tsafta domin dabbobi da makiyayan a faɗin jihar Yobe, kana da samar da isasshen abincin dabbobi da ingantattun allurar riga-kafi da magunguna domin yaqar cutukan da ke addabar dabbobi a ihar.”

Shugaban ƙungiyar, ya ce Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙuduri aniyar farfaɗo da wuraren kiwo da burtaloli da zai bai wa makiyaya damar gudanar da harkokin su ba tare da wata tsangwamar da zata haifar da rikici da manoma ba.

Ya ce kuma gwamnatin jihar ta ɗauki matakan killace burtalolin tare da raya su domin su kasance tabbatattun wuraren kiwo da burtalolin dabbobin domin daqile rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Bugu da ƙari kuma, Hon. Khalil ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni, bisa hoɓɓasar da ya yi wajen ƙulla yarjejeniyar inganta kiwo tsakanin Jihar Yobe da Ƙasar Moroko dangane da shaharar ta a duniya ta fannin kiwon dabbobi tare da samar da nama da madara.

A hannu guda kuma, shugaban ƙungiyar Kulen Allah ya yi kira da babban murya ga makiyaya a faɗin ƙasar nan da cewa su guje wa aikata duk wani abin da zai tayar da zaune tsaye balle zubar da ƙimar ’ya’yan Fulani, mutanen da aka san su da asali, zaman lafiya da mutunci ba ma a Nijeriya kawai ba, a faxin duniya.

A qarshe ya buqaci makiyayan a duk inda su ke su zauna lafiya tsakanin su da manona da sauran abokan zama, sannan su ba gwamnatocin ƙasar nan cikakken goyon baya da haɗin kai a ƙoƙarin da su ke na samar da zaman lafiya da tsaro a Nijeriya.