Ƙungiyar Izala ta shirya wa malamai masu tafsiri taron bita a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Ƙungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a Waikamatus Sunnah JIBWIS a Jihar Gombe, ta shiryawa Malaman da za su gudanar da Tafsirin watan Ramadan taron bita na ƙarawa juna sani.

A jawabin sa babban baƙo a wajen taro, gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, yabawa ƙungiyar ta izala ya yi kan wannan shiri inda ya ce hakan yana da kyau dan jan hankalin malaman daga kaucewa tsarin gudanar da tafsirin su shiga abinda bai shafe su ba.

Gwamna Inuwa, ya ce tun kafuwar ƙungiyar ta izala suke ƙoƙari wajen ilmantar da al’umma muhimmancin nemnan ilimi.

Ganin ƙungiyar na da fili da suke shari’a akai gwamnan a ranar Lahadi, ya miƙawa ƙungiyar satifet ɗin shaidar mallakar mata da filin da ya ke cibiyar kasuwanci ta City Centre kusa da helkwatar hukumar zaɓe ta ƙasa INEC a jihar.

Sannan kuma ya bai wa ƙungiyar ta izala gudumawar kuɗi naira miliyan goma saboda wannan bita da ta shiryawa Malamai masu tafsiri.

Ya miqa satifiket ɗin ne da gudumawar kuɗin ta hannun kwamishinan shari’a na jihar Zubairu Muhammad Umar.

Da yake maida jawabi Shugaban ƙungiyar ta jama’atul izalatil bidi’a wa’ikamatus sunnah JIBWIS na jihar Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe, godewa gwamnatin jihar ya yi kan mallakar mata da wannan fili da kuma kyautar naira miliyan goma.

Injiniya Salisu Gombe, yace a ƙungiyance za su sakawa Gwamnati bisa wannan kyauta da filinsu da ya mallakar su.

Shugaban ya kuma hori Malaman da su guji yada jita- jita musamman na shiga abunda bai shafe su suna ƙeta daraja ko ’yancin wani a lokacin tafsirin azumin watan Ramadan a faɗin ƙananan hukumomin jihar 11 inda ya ce su sani fa suna sa hannu ne a madadin Allah wannan karatu da suke yi.

Mataimakin shugaban majisar malamai ta ƙasa kuma Shugaban Taron Shiek Usman Isa Taliyawa, cewa ya yi kungiyar izala tana shirya irin wannan taron bita ne duk shekara domin ƙara ilmantar da malamai su kuma su ilmantar da masu sauraron su.

Taron ya samu halartar malamai masu wa’azu shugabanin ɓangarori daban-daban da yan agaji da kuma Alarammomi.